Jerin sunayen sojoji 11 da aka binne yau a Kaduna

Jerin sunayen sojoji 11 da aka binne yau a Kaduna

A yau ne, cikin hawaye, aka binne gawar sojoji 11 da aka kashe a kauyen Doka dake karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wasu 'yan bindiga ne suka mamayi dakarun sojin, suka kashe su a ranar 20 ga watan Maris yayin da aka tura su dakile aiyukan ta'addanci da suka hada da satar mutane, satar shanu, fashi da makami da sauransu.

Jerin sunayen sojoji 11 da aka binne yau a Kaduna
Jerin sunayen sojoji 11 da aka binne yau a Kaduna

Sojojin da aka kashe din su ne; Olabode Hammed (jihar Ogun), Bamidele Adekunle (jihar Ogun), Owochukwu Christian Chigoziri (Jihar Ribas), Adamu Muhammed (Bauchi), Lamara Ahmed (Jigawa), Mubarak Suleiman (Filato), Bashir Sani (Katsina), Usman Abubakar Jalo (Gombe), Nafiu Iliyasu (Jigawa), Safiyanu Ahmed (Jigawa)da Alhassan Ibrahim (Kaduna).

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, da kwamandan barikin soji ta daya ya wakilta, Manjo Janar Mohammed Mohammed, ya ce bayyana kashe sojojin a matsayin abin takaici da sadaukar was.

DUBA WANNAN: Ku dawo da kudin da ku ka karba ba bisa ka'ida ba tunda an sanar da alawus din ku - SERAP ta fadawa 'yan majalisar dattijai

Da yake mika sakon ta'aziyya ga iyalan sojojin, Buratai, ya ce jinin sojojin ba zai tafi a banza ba.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i', da sakataren gwamnatin jihar Lawal Balarabe ya wakilta ya yi alkawarin bayar da tallafin N500,000 ga iyalin kowanne daga cikin sojojin tare da yin addu'ar Allah ya ji kansu, ya bawa iyalinsu hakurin jure rashinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng