Ba mu san da lambar yabon da aka ba Shugaban Najeriya ba - Cibiyar King Center
- A farkon makon nan jikokin Martin Luther King su ka Shugaba Buhari kyauta
- Cibiyar da ke kula da ayyukan Marigayin tace ba ta ma san an yi wannan aiki ba
- King Center tace ba ita ta ba Shugaba Buhari kyauta ba kuma ba ta aiki kowa ba
Mun samu labari cewa kwanan nan aka damfari Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari inda aka basa lambar yabo da jinjina na bogi. Har yanzu dai fadar Shugaban kasa ba tayi jawabi game da wannan abin kunya ba.
Idan ku na biye da mu za ku samu labari cewa a makon nan ne Jikokin Marigayi Martin Luther King na kasar Amurka su ka zo Najeriya inda su ka gana Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa watau Aso Villa.
KU KARANTA: Adadin Sanatocin da ke bayan Shugaba Buhari a Majalisa
A ziyarar an ba Shugaban kasa Buhari kyauta a matsayin sa na bakin fata da kuma lambar yabo saboda irin mulkin da yake yi na a zo - a gani a Afrika. Sai dai kuma yanzu mun fara jin labari cewa kyautar karya ce aka ba Shugaban.
Cibiyar king center ta Amurka wanda ke yi wa Marigayi Martin Luther King hidima ta tabbatar da cewa ba ta san da wannan kyauta da aka ba Buhari ba kuma dai babu sa hannun Jikokin Martin Luther King a wajen bada wannan lambar girma.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng