Da karfin tuwo wasu jami'an tsaro cikin farin kaya su ka yi awon gaba da ma'aikacin jaridar Daily Trust
- Jami'an 'yan sanda cikin farin kaya sun yi awon gaba da ma'aikacin jaridar Daily Trust, Abdullahi Musa Krishi, a yau
- Wata majiya ta bayyana cewar jami'an 'yan sanda sun yi amfani da karfin tuwo wajen tafiya da dan jaridar a harabar majalisar tarayya
- Wasu 'yan jarida da su ka yi kokarin dakatar da jami'an tsaron sun ce jami'an tsaron sun gaza nuna takardar shaidar kama shi
Wasu 'yan sanda cikin farin kaya sun yi awon gaba da ma'aikacin jaridar Daily Trust a yau, Talata, a harabar majalisar tarayya.
Rahotanni sun bayyana cewar jami'an 'yan sanda sun ce an ba su umarni ne daga ofishin hukumar 'yan sanda na shiyyar "A" dake Kano.
Wasu 'yan jarida da abin ya faru a kan idonsu sun ce 'yan sandan sun gaza nuna shaidar kama ma'aikacin kuma duk rokon da su ka yiwa jami'an tsaron sandan a kan su yi hakuri bai yi tasiri ba.
An tafi da Krishi ne cikin ankwa bayan jami'an sun bukaci ya nuna katin shaidar aikinsa.
Wasu shugabannin majalisar sun bayyana cewar an tafi da Kirishi Kano sabanin tunanin abokan aikinsa na ganin an tafi da shi ofishin hukumar 'yan sanda dake Abuja.
DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Trump ya kori sakataren wajen Amurka Rex Tillerson
Wata majiya ta ce an kama ma'aikacin jaridar ne saboda wani korafi da gwamnatin jihar Jigawa tayi a kan wani rahoto da ya wallafa. Gwamnatin jihar ta zarge shi da yin batanci gareta.
Hukumar kamfanin jaridar Daily Trust ta ce lauyanta zai ziyarci Kirishi yayin da zai bayyana a gaban mataimakin shugaban 'yan sanda na shiyyar "A" a Kano.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng