Rikicin Makiyaya: Ba dai-dai bane a rika daukan Fulani a matsayin 'yan ta'adda - Atiku
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana bacin ran sa akan yadda ake cin zarafin Fulani a fadin kasar
- Atiku ya ce ba dai-dai bane a rika danganata Fulani da ta'adanci a Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana bacin ran sa akan yadda ake cin zarfin 'yan Fulani a Najeriya da kuma yadda ake musu kallon ‘yan ta’adda a kasar.
Atiku ya ce ba daidai bane a bata al’umma daya, saboda laifin wasu tsiraru daga cikin su
"Bai dace ba a rika amfani da sigar ‘killer herdsmen' (Makiyaya masu kashe-kashe) ko ‘killer Fulani herdsmen’ (Fulani masu kashe-kashe) wajen kiran sunan makiyaya masu tada rikici.
"Idan masu garkuwa da mutanen suka sace mutanen ana kiran su da sunan masu garkuwa da mutane ne ba da sunan kabilar su ba, sabdao haka suma makiyaya masu kasashe bai kamata a kira su da sunan Fulani ba.
KU KARANTA : Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Saleh Michika rasuwa
“Fulani mutanen dake ke son zaman lafiya da sauran kabilu a Najeriya,” Inji Atiku.
Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da wani dan jaridar THISDAY ya tambaye ra’ayin sa game da kashe-kashen da ‘Fulani masu kashe-kashe keyi a faddin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng