Dapchi: Iyayen yan matan da aka sace sun mamaye birnin Abuja

Dapchi: Iyayen yan matan da aka sace sun mamaye birnin Abuja

Iyayen 'yan matan nan su 110 da wadanda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka sace su a garin Dapchi na jihar Yobe sun tura wakillai zuwa birnin tarayya Abuja domin matsa lamba ga gwamnatin tarayya wajen ganin an kwato masu 'ya 'yan su.

Mun samu dai cewa Sakataren kungiyar iyayen mai suna Bukar Kachalla ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin da suke kokarin ganin sun zauna tare da hadewa da shugabannin gangamin nan dake fafutukar ganin an sako 'yan matan Chibok.

Dapchi: Iyayen yan matan da aka sace sun mamaye birnin Abuja
Dapchi: Iyayen yan matan da aka sace sun mamaye birnin Abuja

KU KARANTA: Dalilin da yasa aka ba da belin Maryam Sanda

Legit.ng ta samu haka zalika cewa wakillan kungiyar iyayen 'yan matan sun kuma kai koken su ga 'yan majalisar tarayya inda suka bukaci su tursasawa gwamnatin shugaba Buhari din wajen ganin ya jagoranci sako masu 'ya'ya.

A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi watau Islamic Movement of Nigeria, IMN a turance da aka fi sani da 'yan shi'a sun fita sun tattare wasu manyan hanyoyin garin Abuja suna zanga-zangar neman a sakar masu shugaba.

Mun samu haka zalika cewa zanga-zangar ta su da suke cigaba da yi a saman manyan titunan babbar birnin kasar ta jawo cunkoson ababen hawa sosai inda hakan ne ma ya sanya wasu masu motoci canza hanya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng