Canji: Baitul malin Najeriya ta tumbatsa, ta yi cikar da bata taba yi ba tun mulkin Jonathan - CBN

Canji: Baitul malin Najeriya ta tumbatsa, ta yi cikar da bata taba yi ba tun mulkin Jonathan - CBN

Kawo yanzu dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta bayyana mana cewa kawo yanzu baitul malin kasar Najeriya ta kai dalar Amurka biliyan 43.2, yawan da bata taba yi ba tun kimanin shekaru hudu da suka gabata kamar yadda babban bankin Najeriya ya bayyana a jiya Laraba.

Haka ma dai gwamnan babban bankin Najeriya din Mista Godwin Emefiele ya yi hasashen cewa baitul malin kasar zai iya kaiwa dalar Amurka biliyan 60 kafin shekarar 2019 indai har aka cigaba da tafiya yadda ake yanzu.

Canji: Baitul malin Najeriya ta tumbatsa, ta yi cikar da bata taba yi ba tun mulkin Jonathan - CBN
Canji: Baitul malin Najeriya ta tumbatsa, ta yi cikar da bata taba yi ba tun mulkin Jonathan - CBN

KU KARANTA: Babu ranar kawo karshen rikicin APC na cikin gida

Legit.ng ta samu haka zalika cewa babban bankin ya kuma bayyana tabbacin samun kyakkyawan yanayin tattalin arzikin kasa nan ba da dadewa domin a cewar sa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na aiki tukuru domin tabbatar da hakan.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya da ke zaman shugaban kasar na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya isa birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin halartar taron masu ruwa da tsaki da ke da zummar korar yunwa daga Najeriya karo na uku.

Mun samu dai cewa tsohon shugaban kasar ya hadu da ministan ayyukan gona na gwamnatin Buhari Cif Audu Ogbe da ma sauran gwamnonin shiyyar ta Arewa maso gabas domin tabbatar da samun nasarar shirin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng