Kamaru ta dawo da sojojin Najeriya 4, 'yan sanda 2 da harin Rann ya bazama cikin kasar

Kamaru ta dawo da sojojin Najeriya 4, 'yan sanda 2 da harin Rann ya bazama cikin kasar

- Mayakan kungiyar Boko sun kai wani mummunan hari sansanin soji da na 'yan gudun hijira a garin Rann dake jihar Borno

- Rahotanni sun bayyana cewar, musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar takwas daga cikin dakarun Najeriya

- Wasu rahotannin na nuna cewar dakarun sojin kasar Kamaru sun ceto wata ma'aikaciyar lafiya, Hauwa Mohammed, da mayakan su ka sace

A kalla sojojin Najeriya hudu da 'yan sanda biyu hukumomin kasar Kamaru su ka dawo da su gida Najeriya bayan sun bazama sakamakon wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai sansanin soji dake Rann a jihar Borno.

Kamaru ta dawo da sojojin Najeriya 4, 'yan sanda 2 da harin Rann ya bazama cikin kasar
Kamaru ta dawo da sojojin Najeriya 4, 'yan sanda 2 da harin Rann ya bazama cikin kasar

Sahara Reporters ta rawaito cewar wata majiya a hukumar soji dake Gamboru-Ngala ta tabbatar ma ta da karbar sojin daga hannun askarawan kasar Kamaru.

KU KARANTA: Buhari zai hallarci bikin cikar kasar Ghana shekaru 61

Majiyar ta ce, jami'an sun tsere ne bayan abokan aikin su takwas sun mutu yayin musayar wuta da mayakan kungiyar Boko Haram.

Wata majiyar na nuni da cewar dakarun sojin kasar Kamaru sun ceto wata ma'aikaciyar lafiya Hauwa Mohammed da mayakan su ka yi awon gaba da ita bayan harin. Sai dai babu tabbas dangane da hakan.

Majiyar ta yi ikirarin cewar iyalin Hauwa sun samu labarin sakin ta ne daga mutanen da su ka sace ta.

"Sabon labarin da mu ke da shi shine, an sanar da iyalin Hauwa cewar an ceto ta a kasar Kamaru kuma za a rako ta Maiduguri a yau," a cewar majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel