Nigerian news All categories All tags
Garabasa: Za fara ba da gidan zama ga mazaje masu mata 2 a Hadaddiyar Daular Larabawa

Garabasa: Za fara ba da gidan zama ga mazaje masu mata 2 a Hadaddiyar Daular Larabawa

A wani yunkuri da ta keyi wajen ganin ta rage yawan 'yan mata da zawarawa marasa aure, gwamnatin Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa dake a yankin gabas ta tsakiya ta ayyana shirin ta na fara bayar da tallafin gidan zama ga duk mazan da suka auri mata 2.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin ministan cigaba da kuma samar da ababen more rayuwa na kasar mai suna Dakta Abdullah Belhaif Al-Nuaimi wanda ya sanar da hakan a yayin zaman da majalisar zartarwar kasar ta yi a jiya ranar Laraba.

Garabasa: Za fara ba da gidan zama ga mazaje masu mata 2 a Hadaddiyar Daular Larabawa

Garabasa: Za fara ba da gidan zama ga mazaje masu mata 2 a Hadaddiyar Daular Larabawa

KU KARANTA: Majalisar wakilai sun yi wa ministocin Buhari 2 kaca-kaca

Legit.ng ta tsinkayi minista Dakta Abdullah Belhaif Al-Nuaimi yana cewa ma'aikatar ta sa ta yanke wannan hukuncin ne na bayar da taimakon gida ga masu mata biyu a kasar domin su samu saukin wahalhalun rayuwa.

Haka zalika ya kuma ce, ma'aikatar ta sa za ta bayar da tallafin karkashin shirin samar da gidaje na Shaikh Zayed.

A Najeriya dai a watannin baya ne aka kai wata mata kotun shari'ar musulunci bisa zargin kashe mijin ta saboda ya karo mata kishiya.

A wani labarin kuma, Wata mata mai suna Fatima Mohammad mai shekaru akalla 16 a duniya ta shaidawa wata kotun da ke zama a Abuja yadda tsananin kyaunta ke hana ta zaman lafiya da mijinta mai suna Tasi'u Kasim da suka shafe shekaru biyu tare.

Matar, Fatima Mohammad dai ta doshi kotun ne sannan kuma ta roke ta da ta taimake ta ta raba auren nasu don kuwa a cewar ta tuni zaman lafiya yayi kaura a tare da ita da mijinta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel