Buba Galadima yayi kira ga Jama’a su koma Jam’iyyar NRM
- Buba Galdima ya bada shawara a koma sabuwar Jam’iyya
- Injiniya Galadima yana cikin na hannun dama Buhari a da
- Babban ‘Dan APC yayi kira jama’a su shiga Jam’iyyar NRM
Babban Jigon Jam’iyyar APC mai mulki Injiniya Buba Galadima na nema ya dabawa Jam’iyyar ta su wuka a ciki inda aka same shi yana yi wa sababbin Jam’iyyun da aka kafa kwanaki kamfe a Garin Abuja kwanan nan.
Injiniya Galadima wanda yana cikin amintattun Jam’iyyar APC kuma tsohon jigo a Jam'iyyar CPC, yayi kira ga ‘Yan Najeriya su fita su shiga Jam’iyyar NRM. Jam’iyyar ta NRM kwanan nan aka kafa ta da nufin ceto ‘Yan Najeriya daga kangi.
KU KARANTA: Bukola Saraki na iya rasa kujerar sa a bana
Jaridar Daily Trust ta rahoto Galadima wanda yana cikin na-kusa da Shugaba Buhari a da yana cewa Jam’iyyar ta NRM ta ‘Yan Najeriya ce daga kowane bangare kuma ba ta yarda da nuna son kai da kama-karya ba watau kamr Jam'iyyar APC.
Sanata Muhammadu Saidu Dansadau wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar yayi kaca-kaca da Gwamnatin APC wanda yace ta gaza. Yanzu haka ana fama da matsalar tsaro ta garkuwa da jama’a, sata, fashi da makami da sauran su inji Dansadau.
Jiya mu ka samu labari cewa Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya garzaya Kano wajen daurin aure bayan zaman makoki a Anambra. Mataimakin Shugaban kasa ya gana da manyan ‘Yan siyasar Kano game da rikicin Kwankwasiyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng