Tsohuwa 'yar shekara 83 da shanu 40 gobara ta babbake a jihar Jigawa

Tsohuwa 'yar shekara 83 da shanu 40 gobara ta babbake a jihar Jigawa

- Wata wutar gobara ta babbake tsohuwa 'yar shekara 83 a jihar Jigawa

- Ana zargin wutar ta tashi ne daga wutar jin dumi da tsohuwar ta ajiye a cikin dakinta

- Wata gobarar ta kone gidaje 36 da Shanu 40 a jihar Jigawa

Wata tsohuwa 'yar shekara 83, Malama Sa'adatu Isyaku, dake zaune a kauyen Kwajala dake karamar hukumar Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ta rasa ranta sakamakon afkuwar hatsarin gobara a gidanta.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Abdu Jinjiri, ne ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ofishin hukumar 'yan sanda dake Duste.

Tsohuwa 'yar shekara 83 da shanu 40 gobara ta babbake a jihar Jigawa

Wutar gobara

Jinjiri ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 4:50 na safiyar ranar Asabar, tare da bayyana cewar wutar ta samo asali ne daga wutar jin dumi da dattijuwar ta kai dakinta.

"A yau hukumar 'yan sanda ta samu rahoton cewar wutar gobara ta kone wata tsohuwa, Sa'adatu Isyaku, mai shekaru 83, dake zaune a kauyen Kwajala a karkashin karamar hukumar Dutse. Majiyar mu ta tabbatar mana da cewar gobarar ta samo asali ne daga wutar jin dumi da tsohuwar ta kunna a cikin dakinta. Wutar ta kone dakin tsohuwar da ita gabadaya", inji Jinjiri.

DUBA WANNAN: Mutum biyar sun mutu sakamakon tashin gobara a wani gidan 'yan ci-rani a Makkah

Ya kara da cewar jami'an 'yan sanda sun sun zakulo gawar tsohuwar daga dakin kuma binciken likita a asibiti ya tabbatar da mutuwar ta. Kazalika ya ce an bayar da gawar Sa'adatu ga danginta.

A wani rahoton da NAN ta wallafa, ta ce wata gobarar a kauyen Abanderi dake karamar hukumar ta Dutse ta kone gidaje 36, Shanu 46, da awaki 40, a ranar Litinin da ta gabata.

Jinjiri ya ja hankalin mutanen jihar da su kara kula wajen amfani da wuta musamman a wannan lokaci na hunturu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel