Shugaba Buhari ya halarci Sallar Juma'a tare da gwamnoni
- Rahoto daga mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara, Bashir Ahmed ya nuna cewa na sallami Yusuf Buhari daga Asibiti
- Dan shugaba Buharin dai ya samu hadari ne sanadiyar wasa da babur tare da wani abokinsa a cikin garin Abuja
- Shugaba Muhammadu Buhari ya fito Sallar Juma'a inda ya tarbi gwamnonin jihohin Arewa 4
Shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci Sallar Juma'a a yau Juma'a, 1 ga watan Junairu, 2018 a Masallacin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci fadar a yau sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da gwamnan jihar Bauchi, Mohammad Abubakar.
Ana sa ran cewa gwamnan jihaar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya zo mika godiya ne ga shugaba Buhammadu Buhari game da samun halartan bikin kaddamar da babban tashan sauke kayayyaki na jirgin kasa da kuma kaddamar da sabbin jiragen kasa 10 domin safara tsakanin jihar Kaduna da Abuja.
Hakazalika ana hasashen cewa ya zo neman goyon bayan Buhari akan hutan ana kunno masa a jiharsa sanadiyar koran malamai 21,000 da yayi a jihar bisa ga hujjan cewa basu cancanci koyarwa ba.
KU KARANTA: Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, an sallamo shi daga Asibiti
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng