Tirkashi! Kotu ta ƙwace ma tsohon gwamnan jihar Katsina gidaje 31
Wutar yaki da cin hanci da rashawa na cigaba da ruruwa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda ya alkarwanta, ba sani ba sabo.
Gwamnatin jihar Katsina karkashin Aminu Bello Masari ne ta maka tsohon gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Shehu Shema gaban kotu tare da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, kan zargin karkatar da kudaden al’umma.
KU KARANTA: Rundunar Yansandan jihar Filato tayi nasarar tarwatsa wasu gungun yan fashi da makami
Sakamakon wannan shari’a da ake tayi ne hukumar EFCC ta mika kokon bararta ga babbar kotun tarayya dake garin Abuja, inda ta bukaci kotun data kwace wasu gidajen tsohon gwamnan guda goma sha takwas.
Alkalin kotun, mai shari’a Kolawalole ya karbi bukatar da hukumar EFCC tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya suka nema daga kotunsa, inda ya bada umarnin kwace wasu gidaje guda goma sha takwas mallakin tsohon gwamnan, kamar yadda wani ma’abocin kafar sadarwar Facebook mai suna Aminu Khalil ya bayyana.
Majiyar Legit.ng ta bayyana haka ne ta hanyar daura hoton umarnin kotun, kamar yadda kwamishinan shari’ar jihar Katsina, kuma lauyan gwamnatin jihar Katsina, Ahmad Usman Al-Marzuk ya sanar cikin wata takarda daya sanya ma hannu.
Takardar ta cigaba da fadin cewa ba wannan bane karo na farko da kotu ta kwace kadarorin tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema, inda tace ko a baya ma kotu ta kwace masa gidaje 13, wanda hakan ya kawo adadin gidajen da aka kwace masa zuwa 31.
Gidajen suna jihohin Katsina, Kano, Kadun da Abuja. Sai dai kotun ta kwace gidajen nan ne gabanin ta yanke hukunci akan shari’ar da take saurara, inda bayan yanke hukunci ne za’a tabbatar da kwace gidajen gaba daya, ko akasin haka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ka san wani dan siyasa wand abaya sata, kalla a Legit.ng TV
Asali: Legit.ng