Ba bu wani aibu a auren wuri - Inji wasu iyaye a Najeriya
- An kammala taro kan yadda za’a kawo karshen auren wuri a Yammacin Afrika ta tsakiya
- Wasu iyaye a Najeriya sun goyi bayan auren wuri
- Sunce babu wani aibu a tattare da hakan
A daidai lokacin da ake kammala wani taro kan yadda za’a dakatar da auren wuri a yammacin Afrika ta tsakiya wasu magabata a Najeriya sun goyi bayan auren wurin sunce babu wani aibu tattare da aikata hakan.
A cewar su auren wuri na da matukar tasiri saboda yana hana matasa aikata dabi’ar da bata dace ba.
Malam Muhammad Sadisu Rajab mahaifin yaya mata ne a Najeriya sannan kuma nasa ra’ayin barin auren wuri na kawo matsaloli da suka fi yoyon fitsari illa.
Taron da aka yi a Dakar babban birnin kasar Senegal ya samu halatar shugabannin kungiyoyin agaji, da jami'an gwamnati da shugabannin addinai da na al'umma da kuma hukumomin majalisar dinkin duniya .
KU KARANTA KUMA: Ana shari'a da wanda ake zargi da damfarar Matar Atiku Abubakar
Mahalatan taron na son su hana aurar da yaran mata kafin su kai shekaru 18.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng