Labari cikin Hotuna: Aisha Buhari ta sanya rigar Dalar Amurka 4490 a wajen tarbar shugaban kasar Uganda da uwar gidansa
Binciken masana tufafi ya bayyana cewa uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta sanya tufa ta dalar Amurka 4490 a ranar Jumma'ar da ta gabata yayin tarbar shugaban kasar Uganda da uwar gidansa
A ranar Jumma'ar da ta gabata, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da uwar gidansa Aisha Buhari sun tarbi shugaban kasar Uganda H. E Yoweri Kaguta Museveni a Abuja.
Yayin da uwar gidan shugaban kasar sanye da tufafi na Oscar De La Renta Magnolia Guipure ta karbi bakwancin uwargidan shugaban kasar Uganda Janet Kaata Museveni.
KU KARANTA: Fasto Mbaka ya bayyana ra'ayinsa akan IPOB da Nnamdi Kanu
Binciken masana tufafi sun bayyana cewa rigar da Aisha Buhari ta sanya zuwa wajen tarbar shugaban na Uganda kudin ta sun tashi Dalar Amurka 4, 490, wanda jimillar kudin a kudin Najeriya sun doshi kusan Naira miliyan 1, 650, 000 kenan.
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng