Lokacin yara: Shugaba Buhari cikin raha tare da wasu yara
- An hangi shugaba Buhari yana wasa da wassu yara
- Shugaban kasan ya kasance cikin nishadi tare da yaran
An yada hoton shugaba Muhammadu Buhari yana wasa da yara bisa bayyanannan dalilai.
Yaran sun kasance yaran baya daga cikin iyalensa
Hoton shugaba Buhari yana wasa da wasu yara, Bashir Ahmed, mataimakin shugaban wajen kafofin yada labarai ne ya yada a shafinsa na twitter.
Hoton yana dauke da taken ‘Lokacin Yara’; hoton ya kuma nuna cewa shugaban yana iya kebe lokaci daga cikin lokutan ayyukansa domin shakatawa da kananan yara. An ga yaran tsugune a gaban shugaban Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na ganawar sirri da shugaban kasar Uganda Museveni a Abuja
Abun sha’awa, shugaban ya nuna sifan ban dariya a fuskansa yayinda yake wasa da dan yaro dake gefensa na hagu.
Abu mai kyau ne a ga shugaba Buhari cikin nishadi da kwanciyar hankali duk da abubuwan dake faruwa a kasa.
Kalli rubutun da Bashir Ahmad ya wallaf a shafin twitter a kasa:
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng