Kwallon kafa: Real Madrid ta sullubo daga teburin La-liga
- Barcelona ta sha gaban Real Madrid a Gasar La-liga
- Rashin Dan wasRonaldo ya sa Real Madrid ta yi canjaras
- Real Madrid ta buga 2-2 da Kungiyar Valencia a wasan jiya
Zakarun bara Real Madrid sun sullubo daga teburin La-liga a karshen wannan makon. Tuni Real Socieded tayi sama a teburin.
Hakan ya zo ne bayan Real Madrid ta tashi wasan ta da Valencia 2-2 a cikin daren jiya. Dan wasa mai jini a jika Marco Asensio ne ya fara cin kwallo a wasan kuma ya ceci Real Madrid a karshe. Dan wasan gaba Karim Benzema ya barar da kwallaye da dama a wasan.
KU KARANTA: 'Yan wasan da su ka fi tsada a Duniya
Ba mamaki rashin manyan 'Yan wasa irin su Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos ya sa Real Madrid din ta yi canjaras. Barcelona dai ta lashe wasan ta shekaran jiya tsakanin ta da Kungiyar Alaves da ci biyu da nema. Dan wasa Messi ne ya ci kwallayen sa na farko a kakar bana.
A makon dai Manchester City ta sha da kyar inda tayi nasara a minti ma 97 jiya. Haka ma Chelsea da Manchester United sun doke Everton da Leicester City da ci biyu duk da nema.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Abubuwan dubawa kafuin fara soyayya
Asali: Legit.ng