Messi Ya Ja Tawaga zuwa wajen Trump ana tsaka da Gwabza Yaki da Iran
- Zakaran dan kwallon ƙungiyar Inter Miami da ke Amurka, Lionel Messi ya jagoranci tawaga zuwa wajen Donald Trump a fadar White House
- Shugaba Donald Trump ya yaba wa Messi bisa yadda ya ke taka leda, ya ke samun nasara, kuma ya kwatanta shi gwarzon dan wasan Brazil, Pele
- Ziyarar da Messi da 'yan tawagar shi suka kai White House ta zo ne a daidai lokacin da Amurka da Isra'ila ke cigaba da gwabza yaki da Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Lionel Messi tare da abokan wasansa na ƙungiyar Inter Miami sun gana da Shugaban Amurka, Donald Trump a Fadar White House.
Inter Miami ta lashe wasan ƙarshe na gasar babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka wato MLS a karon farko a watan Disamban 2025 da ya gabata.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa kulob ɗin ta samu gayyatar zuwa Fadar White House kafin wasan MLS da za su buga da DC United a birnin Washington ranar Asabar.
Lionel Messi ya hadu da Donald Trump
Messi da sauran abokan wasansa sun tsaya a kan dandalin taron yayin da Trump ke jawabi ga manema labarai, inda ya taya su murnar nasarar bayan ya yi bayani kan hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kaiwa Iran a halin yanzu.
Trump ya ce:
“Ɗana Barron ya ce mani, ‘Baba, ka san wanda zai zo nan yau?’ Sai na ce masa, ‘A’a, ina da abubuwa da yawa da nake yi.’
“Sai ya ce, ‘Messi!’ Shi babban masoyinka ne. Yana ganin kai mutum ne mai girma, kuma ina ganin kun taɓa haɗuwa a baya.”
Yadda Trump ya kwatanta Messi da Pele
Da yake magana kai tsaye ga Messi, Trump yaba wa dan wasan bisa yadda ya shafe shekaru yana samun nasara a kulob daban-daban.
Shugaba Trump ya ce:
“Leo ya lashe kofinsa na 47 a wannan gagarumar sana’ar tasa – wanda shi ne mafi yawa a tarihi.
“Duk da za ka iya zuwa ko wace ƙungiya a duniya, ka zaɓi Miami. Na gode maka kwarai.”

Source: Getty Images
Rahoton Yahoo Sports ya nuna cewa Trump ya ƙara da cewa:
“Bai kamata in faɗi haka ba saboda na tsufa, amma na taɓa kallon Pele yana wasa. Ban sani ba, watakila kai ma ka fi Pele. Amma Pele ma ya kasance ƙwararren ɗan wasa sosai.”
Shugaba Trump ba zai tura soja Iran ba
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ba zai tura sojojin kasa zuwa Iran ba a yakin da ake gwabzawa.
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya fadi haka ne yayin hira da shi bayan shafe kwana 7 ana fafata yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran.
Ya yi ikirarin cewa ya ruguza wurare da dama a Tehran saboda haka ba shi bukatar tura sojoji duk da cewa Iran ta ce za ta yi maganin duk wanda ya turo.
Asali: Legit.ng
