Messi Ya Gindaya Tsauraran Sharudda na Taka Leda Tare da Osimhen a Galatasaray

Messi Ya Gindaya Tsauraran Sharudda na Taka Leda Tare da Osimhen a Galatasaray

  • Lionel Messi na shirin komawa kungiyar Galatasaray ta Turkiyya domin buga wasa tare da dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen
  • Tsohon ɗan wasan na Barcelona ya gindaya sharadin cewa zai buga wasanni 12 ne kawai a birnin Istanbul ba tare da buga wasan waje ba
  • Yanzu haka Galatasaray tana tattaunawa da wakilan Messi don ganin ya dawo Turkiyya kafin a fara gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Turkiyya - Rahotanni daga ƙasar Turkiyya sun bayyana cewa shahararren ɗan wasa Lionel Messi na iya komawa Galatasaray a matsayin aro na gajeren lokaci.

Idan wannan ciniki ya tabbata, Messi zai buga wasa tare da fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, a ƙungiyar ta Turkiyya.

Messi ya gindaya sharuddan buga wasa a Galatasaray gabanin gasar kofin duniya.
Lionel Messi a cikin fili, da dan wasan Najeriya, Vicitor Osimhen na kungiyar Galatasary. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, yana hutu ne a halin yanzu kafin fara sabuwar kakar wasan MLS, a cewar rahoton Punch Sport Extra.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya hallara taron sarakunan Afrika, ba a ga Aminu Ado ba

Messi ya kafa sharuddan shiga Galatasaray

Tsohon ɗan wasan na Barcelona yana neman hanyar da zai kasance cikin ƙoshin lafiya kafin fara gasar cin kofin duniya ta 2026.

Fitaccen mai sharhi kan wasanni, Levent Tüzemen, ya bayyana cewa Galatasaray ta fara tattaunawa da wakilan ɗan wasan na Argentina.

Tüzemen ya bayyana cewa Messi ya yarda zai buga wasanni 12 a cikin watanni huɗu, muddin dukkan wasannin za su gudana ne a Istanbul.

Hakan na nufin Messi ba zai buga wasannin waje ba, inda yake son buga wasanni ne kawai a filin wasa na RAMS Park.

Tüzemen ya ce:

“Messi ya bayyana cewa ba ya son zuwa gasar cin kofin duniya da rauni a jikinsa, saboda haka yake son buga wasanni masu sauƙi.”

Haduwar Messi da Osimhen a Galatasaray

Wannan mataki zai sa Messi ya buga wasa tare da Osimhen, wanda ya zama babban ɗan wasa a ƙungiyar tun komawarsa.

Osimhen ya taimaka wa Galatasaray lashe kofuna biyu a kakar 2024/25, inda ya zura ƙwallaye 37 a wasanni 47 da ya buga.

Kara karanta wannan

Bayan zama sojan Rasha, 'dan Kano ya rasu yana gwabza yaki da Ukraine

Shigowar Messi zai ƙara wa ƙungiyar ƙarfin da take buƙata domin lashe gasar cin kofin Turkiyya inda take saman teburi.

A halin yanzu, Galatasaray tana matsayi na daya da maki 49, inda ta ba Fenerbahce tazarar maki uku yayin da ake da ragowar wasanni 14, in ji rahoton ESPN.

Lionel Messi ya ce ba zai buga wasannin waje ba, kuma zai taka leda ne na watanni 4 kadai a Galatasary
Shaharadden dan wasan kwallon kafa, Lionel Messi na murna bayan ya zura kwallo a raga. Hoto: @leomessi
Source: Instagram

Shirye-shiryen karɓar Messi a Turkiyya

Masu sharhi sun bayyana cewa idan Messi ya isa Turkiyya, sama da mutane miliyan ɗaya za su tarbe shi a filin jirgi.

Tüzemen ya bayyana cewa tuni ƙungiyar Al Hilal ta nemi Messi, amma ya ƙi amincewa da tayin nasu domin zuwa Turkiyya.

Galatasaray tana da wasanni shida na gida a gasar lig, da wasan kofin Turkiyya guda ɗaya, da kuma wasan Juventus a gasar zakarun Turai.

Har yanzu ba a tabbatar ko Messi zai yarda ya yi tafiya zuwa ƙasar Italiya domin buga wasan share fage da Juventus ba.

Idan aka cimma yarjejeniyar, duniyar ƙwallon ƙafa za ta zura ido domin ganin yadda Messi da Osimhen za su lalata gidan baya na abokan hamayya.

Kara karanta wannan

An hango sauki: Ana so Tinubu ya sa tallafin danyen mai, a rage kudin fetur

Real Madrid na son sayen Osimhen

A wani labarin, mun rahoto cewa, Real Madrid na shirin sayen ɗan wasan Super Eagles, Victor Osimhen, daga Galatasaray kan kuɗi sama da euro miliyan ɗari.

Wannan matakin na daga cikin shirin ƙungiyar na sake karfafa gabansu da kuma ba Kylian Mbappé damar komawa matsayinsa na mai buga hagu.

Madrid na ganin lokaci ya yi da za ta dawo da cikakken ɗan gaba mai kwarewar zura ƙwallo, gudu da kuma iya buga finareti, kamar dai dan gaban Najeriya, Osimhen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com