Kasashen da Suka Fi Lashe Gasar Cin Kofin AFCON a Tarihi da Shekarun da Suka Yi Nasara

Kasashen da Suka Fi Lashe Gasar Cin Kofin AFCON a Tarihi da Shekarun da Suka Yi Nasara

Rabat, Morocco - Tawagar Teranga Lions ta kasar Senegal ta samu nasarar lashe gasar cin kofin nahiyar (AFCON) na shekar 2025.

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Nasarar da ƙasar Senegal ta samu a wasan karshe na AFCON 2025, inda ta doke kasa mai masaukin baki Morocco cikin kayatarwa, ta sake sauya fasalin tarihin kwallon kafa a Afirka.

Kasashen da suka fi lashe gasar AFCON
Kofin cin gasar nahiyar Afrika (AFCON) Hoto: @CAF_Online
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro kasashen da suka fi lashe kofin AFCON a tarihin gasar wadda aka fara bugawa a shekarar 1957.

Kasar Senegal ta lashe gasar AFCON 2025

Rahoton tashar Aljazeera ya ce tawagar Teranga Lions ta kasar Senegal ta samu nasarar doke takwararta ta Atlas Lions ta kasar Morocco a wasan karshe na AFCON 2025.

Nasarar da Senegal ta samu a birnin Rabat bayan karin lokaci ta kawo karshen burin Morocco na ɗaga kofin AFCON a gida.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: An 'gano' inda 'yan ta'adda ke tserewa saboda ruwan wuta a Sokoto

Har ila yau nasarar ta tabbatar da karfafa matsayin Senegal a matsayin sabuwar kasa mai tasiri a kwallon Afirka ta zamani.

Da wannan nasara, hankula sun sake karkata zuwa jerin kasashen da suka fi lashe AFCON a tarihi.

Wace kasa ta fi lashe AFCON a tarihi?

Tashar ESPN ta ce kasar Egypt ce ke kan gaba a tarihin AFCON, inda The Pharaohs suka lashe kofin sau bakwai, ciki har da gasar farko ta shekarar 1957.

Ƙasashe bakwai kuma sun lashe kofin fiye da sau ɗaya, yayin da jimillar kasashe 15 ne suka taɓa lashe AFCON tun farkon fara buga gasar.

Ga jerin kasashen da suka fi lashe kofin AFCON, tare da tarihin nasarorinsu:

1. Egypt – sau 7

Egypt ce kasar da ta fi kowace nasara a tarihin AFCON, inda ta gina wannan tarihi tsawon shekaru da dama, shafin Sportingnews ya tabbatar da hakan.

Sun lashe kofinsu na farko a 1957, sannan suka nuna kwarewa ta musamman tsakanin 2006 zuwa 2010, lokacin da suka lashe gasar sau uku a jere.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika sako mai dadi ga 'yan wasan Najeriya bayan sun lallasa Masar a gasar AFCON

Ana danganta nasarorinsu da tsari mai kyau, kakkarfan gasar cikin gida da kuma iya jure matsin lamba.

Egypt ta lashe gasar AFCON a shekarun 1957, 1959, 1986, 1998, 2006, 2008, 2010

2. Cameroon – sau 5

Cameroon na matsayi na biyu da kofuna biyar. Tawagar Indomitable Lions sun yi tashe a shekarun 1980, 1990 da farkon 2000, tare da fitattun ’yan wasa kamar Roger Milla da Samuel Eto’o.

Karfinsu, salon kai hari da jarumta a wasannin AFCON sun sa su zama abin tsoro ga sauran kasashe.

Kasar Cameroon ta lashe kofin AFCON sau biyar a tsakanin shekarun 1984, 1988, 2000, 2002 sai kuma a 2017 wanda shi ne lokacin karshe da ta yi naara.

3. Ghana – sau 4

Ghana ta lashe AFCON sau huɗu, abin da ya nuna matsayinta a matsayin ɗaya daga cikin manyan kasashen kwallo a Afirka.

Tawagar Black Stars sun mamaye gasar AFCON a shekarun 1960 da farkon 1980, suna da salon wasa mai kwarewa da dabaru.

Kasar Ghana ta samu nasarar lashe kofin AFCON sau hudu a tsakanin shekarun 1963, 1965, 1978 da 1982.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta tuna da Super Eagles bayan rashin nasara a hannun Morocco

Ko da yake ba su yi nasara a ’yan shekarun nan ba, Ghana na ci gaba da zama babbar kasar da ake ji da ita a fannin kwallon kafa a Afrika.

4. Najeriya – sau 3

Najeriya ta lashe kofin AFCON sau uku, abin da ke nuna tasirinta a kwallon Afirka.

Tawagar Super Eagles sun lashe kofin a 1980, 1994 da 2013, inda kowace nasara ta wakilci sabon zamani na ’yan wasa.

A gasar AFCON ta 2025 da aka kammala, tawagar Super Eagles ta lashe kyautar tagulla bayan ta zo ta uku.

5. Ivory Coast – sau 3

Kasar Ivory Coast da ke Yammacin Afrika ta lashe AFCON sau uku a shekarun 1992, 2015 da 2023.

Nasarorinsu sun samo asali ne daga samun jajirtattun 'yan wasa da suka haɗa da Didier Drogba da Yaya Touré.

Duk da shan kaye a wasannin karshe na AFCON sau da dama, nasarorin nasu sun nuna juriyarsu da kwazo.

6. Senegal – sau 2

Nasarar Senegal a kan Morocco ta sanya su cikin jerin ƙasashen da suka lashe AFCON sau biyu.

Senegal ta lashe kofin AFCON 2025
'Yan wasan Senegal na murnar lashe kofin AFCON 2025 Hoto: @CAF_Online
Source: Twitter

Bayan lashe kofinsu na farko a 2021, Tawagar Teranga Lions ta tabbatar da cewa wannan nasara ba ta zo ne bisa sa’a kawai ba.

Kara karanta wannan

Bayan Morocco ta doke Najeriya, BUA ya yi magana kan alkawarin Dalolin kudi da ya yi

Tare da tsaro mai karfi, tsari da hazikan ’yan wasa, Senegal na nuna alamun zama sabuwar babbar kasa da za ta iya kalubalantar tsofaffin manyan kasashe a Afirka.

Najeriya ta gamu da cikas a AFCON 2025

A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar Super Eagles ta Najeriya ta gamu da cikas yayin da take shirin buga wasan kusa dana karshe a gasar AFCON 2025.

Kyaftin ɗin Super Eagles kuma babban ɗan wasan tsakiya, Wilfred Ndidi, bai buga wasan kusa da na karshe da suka fafata da kasar Morocco ba.

Wilfred Ndidi ya samu dakatarwar wasa ɗaya ne sakamakon tara katin gargadi guda biyu (yellow cards) a lokacin wasannin da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng