AFCON 2025: Kocin Morocco Ya Fadi Sunayen 'Yan Wasan Najeriya 3 da Yake Tsoro

AFCON 2025: Kocin Morocco Ya Fadi Sunayen 'Yan Wasan Najeriya 3 da Yake Tsoro

  • Kocin Morocco Walid Regragui ya bayyana Victor Osimhen da 'yan wasan Najeriya biyu a matsayin manyan barazana ga kasarsa
  • Regragui ya nuna jin dadinsa kan rashin Wilfred Ndidi amma ya gargadi yan wasan Moroko cewa su yi hattara da Najeriya a wasansu na yau
  • Onyedika ne ake sa ran zai maye gurbin Ndidi yayin da da Najeriya da Morocco za su fafata a wasan kusa da karshe na gasar AFCON

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Morocco - Kocin tawagar Atlas Lions ta Morocco, Walid Regragui, ya bayyana manyan ’yan wasan da yake fargaba a tawagar Super Eagles ta Najeriya.

Walid Regragui ya bayyana hakan ne yayin da ƙasashen biyu ke shirin fafatawa a wasan kusa da na ƙarshe na gasar AFCON 2025 a daren yau Laraba, 14 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Morocco ta gamu da babbar matsala tana shirin karawa da Najeriya

Kocin Morocco, Walid Regragui ya ce yana tsoron Osimhen, Lookman, gabanin karawarsu a yau.
Kocin Morocco, Walid Regragui, da 'yan wasan Super Eagles na Najeriya. Hoto: @CAF_Online
Source: Twitter

Kocin Morocco na tsoron 'yan wasan Najeriya

Kocin na Morocco ya nuna cewa ko da yake yana murnar rashin kyaftin din Super Eagles, Wilfred Ndidi, amma har yanzu Najeriya tana da miyagun ’yan wasan gaba, in ji rahoton Pulse Sport.

A yayin taron manema labarai da ya gudana a birnin Rabat, Regragui ya ambaci Victor Osimhen, Ademola Lookman, da Alex Iwobi a matsayin manyan barazana ga tsaron bayan tawagar Morocco.

Lookman da Osimhen sun taka rawar gani wajen zura ƙwallaye 13 daga cikin 14 da Najeriya ta ci a wannan gasar ta 2025, inda Lookman ke da hannu a ƙwallaye bakwai, shi kuma Osimhen yana da guda shida.

"Rashin Ndidi zai taimaki Morocco" — Regragui

Kocin na Morocco ya yarda cewa rashin Wilfred Ndidi, wanda aka dakatar saboda katin gargaɗi biyu, zai rage wa Najeriya ƙarfi a tsakiyar fili, amma hakan ba yana nufin wasan zai yi sauƙi ba.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: An fadawa Najeriya abin da za ta yi don doke Morocco a 'semi finals'

"Rashin Ndidi zai taimake mu, amma idan kana da Osimhen, Lookman, da Iwobi, sannan ka duba bencin su, to za ka ga suna da ƙarfi sosai.
"Dole ne mu kiyaye kada mu sakankance kamar yadda muka yi da Kamaru, domin wadannan (Najeriya) za su iya hukunta mu sosai."

— Walid Regragui.

Regragui ya ƙara da cewa dole ne Morocco ta ƙara kaimi a zagaye na biyu na wasan domin kada su ba wa Najeriya damar numfashi ko amfani da gwanintarsu ta sarrafa ƙwallo.

Ana sa ran wasan Najeriya da Morocco zai dauki zafi a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON 2025.
Tawagar 'yan wasan Atlas Lion ta Morocco da tawagar Super Eagles ta Najeriya. Hoto: @lionsdelatlass, @NGSuperEagles
Source: Twitter

Raphael Onyedika zai maye gurbin Ndidi

Sakamakon rashin Ndidi, ana sa ran ɗan wasan tsakiya na Club Brugge, Raphael Onyedika, shi ne zai fara wasan a yau, a madadin kyaftin din Najeriya, in ji rahoton All Nigeria Soccer.

Wannan ne zai zama karo na biyu da Onyedika zai fara wasa a wannan gasar, inda aka ɗora masa nauyin toshe gurbin da babban kyaftin ɗin ya bari domin fuskantar ƙalubalen da Morocco za ta gabatar a gida.

Wasan zai gudana ne da ƙarfe 9:00 na dare agogon Najeriya a filin wasa na Prince Moulay Abdallah, inda dukkan ƙasashen biyu ke neman gurbin shiga wasan ƙarshe.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Abin da muka sani game da Laryea, alkalin wasan Najeriya da Morocco

Kalubalen da Morocco za ta fuskanta

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, babban ɗan wasan tsakiyar kungiyar Atlas Lions ta Morocco, Azzedine Ounahi, ba zai buga wasansu da Najeriya ba.

Kocin Morocco, Walid Regragui ya ce, har yanzu Ounahi, ɗan shekara 25, bai warke daga raunin da ya samu da ya hana shi buga wasannin zagaye na 16 da na Camaroon ba.

Wannan sanarwa ta zo ne a matsayin babban kalubale ga kasar mai masaukin baki, duba da irin muhimmancin da dan wasan yake da shi a tsarin wasan Regragui.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com