Tofa: Osimhen na Barazanar Barin Super Eagles Ana tsaka da Wasannin AFCON 2025
- Tauraron dan wasan gaba, Victor Osimhen ya yi barazanar daina buga wa Super Eagles wasa bayan hatsaniyarsa da Ademola Lookman
- Osimhen ya fusata ne bayan Lookman da Bruno Onyemaechi suka zaɓi yin wasan nuna gwaninta maimakon ba shi ƙwallo ya zura a raga
- Rahoto ya nuna matakin da hukumar kwallon kafar Najeriya ta dauka yayin da Super Eagles ke shirin fafatawa da Jamhuriyyar Congo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Morocco - Duk da nasarar da Super Eagles ta samu na lallasa Mozambique da ci 4-0 don samun gurbin zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar AFCON, wani babban rikici ya kunno kai a kungiyar.
An rahoto cewa tauraron ɗan wasan gaba, Victor Osimhen, ya yi barazanar yin murabus daga buga wa Super Eagles wasa baki ɗaya bayan wani rikici da ya faru tsakaninsa da Ademola Lookman a lokacin wasan.

Source: Getty Images
Wannan dambarwa ta fara ne a fili a lokacin da Najeriya take tsaka da nuna bajinta a wasan ranar Litinin, 5 fa watan Janairu, 2025, kamar yadda rahoton Arise News ya nuna.
AFCON 2025: Rigimar Osimhen da Lookman
Ko da yake Osimhen da Lookman sun nuna haɗin kai a farkon wasan, inda Lookman ya taimaka wa Osimhen zura ƙwallo ta farko a minti na 47, al'amura sun lalace bayan nan.
Osimhen ya nuna tsananin fushinsa lokacin da ya ga wasu damarmaki na cin ƙwallo suna lalacewa saboda Lookman da Bruno Onyemaechi sun zaɓi yin wasan nuna gwaninta maimakon ba shi ƙwallo ya zura a raga.
A daidai lokacin da Lookman ya nufi wurin buga ƙwallon kusurwa, Osimhen ya tunkare shi cikin fushi, yana nuna masa yatsa a fuska.
Kyaftin ɗin ƙungiyar, Wilfried Ndidi, ya yi ƙoƙarin shiga tsakani domin kwantar da hankula, amma Osimhen ya buge hannun Ndidi cikin fushi.
Wani abin mamaki shi ne yadda ɗan wasan baya na Mozambique, Reinildo, ya zama wanda ya raba fadan 'yan wasan, kamar yadda wakilin Legit Hausa ya gani a lokacin wasan.
Daga nan, Osimhen ya yi wa koci, Eric Chelle alama cewa yana son a canza shi, inda kocin ya maye gurbinsa da Moses Simon duk da cewa Najeriya tana gaba da ci 3-0.
Barazanar Osimhen ta barin Super Eagles
Bayan tashi wasan, maimakon ya shiga murnar nasara da takwarorinsa suka yi a tsakiyar fili, Osimhen ya wuce kai-tsaye zuwa hanyar da ke kai wa ɗakunan canja sutura, in ji rahoton Goal.com.
Rahotanni sun nuna cewa ya bar filin wasan cikin gaggawa, ya jefar da katin shaidar ɗan wasa, tare da sanar da jami'an ƙungiyar cewa "ya gama" da Super Eagles kuma zai koma ƙungiyar sa ta Galatasaray da ke Turkiyya.
Wannan danyen hukunci ya girgiza sansanin ’yan wasan, inda aka ga Osimhen zaune shi kaɗai a cikin motar tawagar yayin da sauran ’yan wasan ke ganawa da manema labarai.

Source: UGC
Ƙoƙarin sasanta rikicin da matsayin NFF
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ya fara tattaunawa da Osimhen domin kwantar masa da hankali, duba da muhimmancin sa ga tawagar.
Sai dai wasu jami'an hukumar suna ganin cewa halin ɗan wasan na nuna fushi a fili yana shafar haɗin kan ƙungiyar a cewar rahoton Pulse Sport.
Wannan ba shi ne karon farko da Osimhen ke nuna fushi a fili ba, amma wannan karon lamarin ya fi muni domin Lookman ne ya fi kowa haskawa a gasar da gudunmawar ƙwallaye bakwai.
Yayin da Najeriya ke shirin fuskantar ƙasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC) a zagaye na gaba, dukkan idanu suna kan kocin ƙungiyar don gani ko zai iya sasantawa tsakanin waɗannan manyan taurari biyu.
An saka kudi ga 'yan wasan Najeriya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta yi wa Super Eagles alkawarin $10,000, kusan N14m, kan kowace kwallo da za su ci a wasan da za su fafata da Mozambique.
Super Eagles za ta kara da tawagar Mambas ta Mozambique a wasan zagaye na 16 na gasar cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) 2025 a ranar Litinin, 5 ga Janairun 2026.
'Yan kwallon Super Eagles sun kammala wasannin rukuni na gasar da cikakkiyar nasara, inda suka lashe dukkan wasanninsu tare da cin kwallaye takwas.
Asali: Legit.ng


