Bayan Ya Fadi Wasu Kalamai, Man United Ta Kori Kocinta, Ta Maye Gurbinsa Nan Take

Bayan Ya Fadi Wasu Kalamai, Man United Ta Kori Kocinta, Ta Maye Gurbinsa Nan Take

  • Manchester United ta raba gari da mai horar da manyan 'yan wasanta, Ruben Amorim bayan ya shafe watanni 14 a kulob din
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan Amorim ya jagoranci Man United a wasan da kungiyar ta yi kunnen doki 1 - 1 da Leeds United
  • An samu banbancin ra'ayi tsakanin magoya bayan kungiyar Man United kan sallamar kocin, dan asalin kasar Portugal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Manchester, UK - Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kori babban kocinta, Ruben Amorim, bayan shafe watanni 14 yana rike da mukamin mai horar da 'yan wasanta.

Man United, wacce ke fafatawa a gasar cin kofin Firimiya na kasar Ingila ta mika godiyarta ga Amorim bisa gudummuwar da ya bayar a tsawon lokacin da ya shafe yana aiki.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: An saka kudi ga 'yan Super Eagles kan zura kwallo a wasansu da Mozambique

Kocin Manchester United.
Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ruben Amorim Hoto: Manchester United
Source: Getty Images

Man United ta tabbatar da haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo da safiyar yau Litinin, 5 ga watan Janairu, 2025.

Kungiyar Man United ta kori Ruben Amorim

Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ya taso kwanan nan tsakanin kulob din da kocin ne ya janyo tangarda a dangantakarsu, lamarin da ya kai ga korar Amorim daga aikinsa.

Manchester United ta tashi kunnen doki 1–1 da kungiyar kwallon kafa ta Leeds United a ranar Lahadi a filin wasa na Elland Road.

Ana zargin Amorim da sukar wasu daga cikin manyan jami’an kulob din a yayin taron manema labarai bayan tashi daga wannan wasan.

An ce ya bayyana cewa yana bukatar karin iko a harkokin tafiyar da kungiyar, tare da cewa a shirye yake ya bar kulob din idan kwantiraginsa ya kare nan da watanni 18 masu zuwa.

Man United ta nada kocin rikon kwarya

Kara karanta wannan

Ana ta tambayoyi bayan hango tambarin Grok a hoton Tinubu a Faransa

Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United, Darren Fletcher, shi ne zai karbi ragamar jagorancin kungiyar a matsayin kocin rikon kwarya.

An sha sukar Ruben Amorim saboda kin sauya salo da tsarin wasansa, abin da aka danganta da shan kashin da Manchester United ta yi a wasan karshe na gasar Europa League a bara.

Amorim
Wasu 'yan wasan Manchester United da tsohon mai horar da su, Ruben Amorim Hoto: @ManchesterUnited
Source: Getty Images

Ra'ayoyin wasu magoya bayan Man United

Abubakar Nakowa, wani masoyin Man Utd a Katsina, ya shaida wa Legit Hausa cewa ya jima yana dakon lokacin da za a kori Amorim daga kulob din.

"Wallahi ni tun bara na so a kore shi amma kuma a yanzu ya gyara, ya dauko hanyar gina tawaga mai karfi, duk da haka na ji dadin korarsa, ya tafi can mun gode," in ji shi.

Haka nan wani mai goyon bayan Manchester United, Usman Sulaiman ya fadawa wakilinmu cewa a iya hasashensa, korar kocin babban kuskure ne.

Matashin ya ce:

"A labaran da suka fito daga shekaran jiya zuwa yau, Amorim ya fi shugabannin Manchester gaskiya, kuma a tunani tunda suka iya hakuri a kakar da ta wuce, bai kamata su kore shi ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

Ahmed Musa ya yi ritaya a Super Eagles

A wani rahoton, kun ji cewa Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga bugawa tawagar Najeriya wasa bayan shafe shekaru 15 yana wakiltar kasar a wasanni daban-daban.

Fitaccen dan wasan, wanda ya fara taka leda a tawagar Super Eagles a shekarar 2010, shi ne dan wasan da ya fi kowa yawan buga wa Najeriya wasa a matakin manya.

Musa ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai koma gefe, ya ba wasu dama a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262