Gwamnan APC Ya Yi Martani kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Tura Sako ga 'Yan Adawa

Gwamnan APC Ya Yi Martani kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Tura Sako ga 'Yan Adawa

  • Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya yi kalamai bayan samun nasarar da ya yi a Kotun Ƙoli
  • Monday Okpebholo ya yi na'am da hukuncin kotun wanda ya tabbatar da shi a matsayin sahihin gwamnan jihar
  • Gwamnan ya nuna godiyarsa ga ɓangaren shari'a da al'ummar Edo bisa juriya da suka nuna yayin da ake sauraron ƙarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya yi martani kan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da nasararsa a zaɓe.

Gwamna Okpebholo ya yaba da hukuncin Kotun Kolin wanda ya tabbatar da shi a matsayin sahihin gwamnan jihar Edo.

Monday Okpebholo ya ji dadin hukuncin Kotun Koli
Gwamna Okpebholo ya yaba da hukuncin Kotun Koli Hoto: @m_akpakomiza
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Fred Itua, ya fitar a ranar Alhamis, 10 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Kotun Kolin Najeriya ta raba gardama kan batun tsige gwamnan APC daga mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Okpebholo ya yaba da hukuncin kotu

Ya bayyana hukuncin a matsayin hukunci mai muhimmanci wanda ya kawo ƙarshen duk wata gardama ta shari’a da ta taso daga zaɓen gwamnan Edo na shekarar 2024.

Okpebholo ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ta musamman ga kansa da kuma muhimmin lokaci ga ɗaukacin al’ummar jihar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Gwamna Okpebholo ya bayyana matuƙar godiya ga ɓangaren shari’a da kuma jama’ar jihar Edo bisa goyon baya da jajircewarsu a lokacin da ake shari’ar.

"Sakamakon hukuncin Kotun Kolin Najeriya a yau ya tabbatar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin sahihin gwamnan Jihar Edo, kuma hakan ya kawo ƙarshen dukkan ƙarar zaɓe da ta biyo bayan zaɓen gwamna na 2024."
"Wannan hukunci mai ƙarfi ba wai nasara ce ta shari’a kawai ba, amma wata babbar shaida ce da ke sake tabbatar da amincewar jama’ar jihar Edo da suka ba shi dama. Wannan na nuni da fara sabon babi da aka gina kan haɗin kai, haɗa kan al’umma, da ci gaba."

Kara karanta wannan

Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

"Mai girma, Gwamna Monday Okpebholo, yana miƙa godiya mai zurfi ga ɓangaren shari’a bisa jarumta da adalcinsu, da kuma ga jama’ar jihar Edo bisa juriya, haƙuri, da amincewar da suka nuna ga dimokuraɗiyya."

- Fred Itua

Gwamnan Edo ya magantu kan huku
Gwamna Okpebholo ya yi murna da hukuncin Kotun Koli Hoto: @m_akpakomiza
Source: Twitter

Gwamna Okpebholo ya miƙa saƙo ga ƴan adawa

A cikin wani matakin sasanci, gwamnan ya buƙaci abokan hamayyarsa na siyasa da su zo a haɗa kai duk da bambancin jam’iyya.

"Domin nuna dattako, Gwamna Okpebholo yana kira ga dukkan abokan hamayyarsa da mambobin jam’iyyun adawa."

"Zaɓe ya wuce lokaci ne na gudanar da mulki. Ya buƙaci shugabannin siyasa daga kowace jam’iyya da su fito daga ƙangin rarrabuwar kawuna su ba da gudummawa wajen gina jihar Edo mai ƙarfi da cigaba."

- Fred Itua

Gwamna Okpebholo ya yi wa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu alƙawari kan zaɓen 2027.

Gwamna Okpebholo ya yi wa Tinubu alƙawarin samun ƙuri'u miliyan 2.3 a babban zaɓen shekarar 2027 a jihar.

Ya nuna cewa zai yi hakan ne domin rama biki kan ƙauna da kulawar da Shugaba Tinubu yake nunawa jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng