An Samu Rudani kan Rasuwar Dan Wasan Najeriya a Kasar Waje
- Rundunar ‘yan sandan Uganda na bincike kan mutuwar dan kwallon Najeriya, Abubakar Lawal, wanda aka ce ya fado daga bene na uku
- Lawal yana ziyarar wata budurwa ‘yar Tanzaniya a dakin da take zama a katafaren kasuwa a Kampala, daga baya aka same shi a kasa
- Kungiyoyin Vipers SC da Kano Pillars sun nuna alhinin mutuwarsa, yayin da ake kira ga gwamnati ta Najeriya ta binciki abin da ya faru da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kampala, Uganda - Rundunar ‘yan sandan Uganda ta fara bincike kan mutuwar dan wasan Najeriya, Abubakar Lawal.
Rahotanni sun tabbatar da marigayin ya fado daga bene na uku a wata kasuwa da ke birnin Kampala a kasar Uganda.

Asali: Facebook
Menene dalilin mutuwar dan wasa Najeriyan?
Dan wasan mai shekara 29, wanda tsohon dan kwallon Najeriya U-20 ne, yana taka leda a kungiyar Vipers SC kamar yadda shafin Facebook na Uganda Police Force ya wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa ya kai ziyara ne wurin wata budurwa ‘yar Tanzaniya a dakin da take zama a kasuwar Voicemall.
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro na duba bidiyon CCTV da kuma bincike don gano abin da ya faru kafin faduwarsa.
Budurwar marigayin ta yi magana kan lamarin
Budurwarsa, Omary Naima, ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta bar shi a dakin yana hada shayi, amma daga baya an same shi a kasa da misalin 8:00 na safe.
Rahoton ‘yan sanda ya bayyana cewa tsohon dan wasan Najeriya ya iso kasuwar da motarsa mai lamba UBQ 695G don ganin budurwarsa Omary Naima, wacce take dakin 416.
Naima ta ce ta bar Lawal a daki, amma daga baya ta ji cewa ya fado daga baranda, lamarin da ke kara jawo tambayoyi.
An gaggauta kai shi asibitin Entebbe Referral, a nan likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.
Kungiyar Vipers SC ta fitar da sanarwa, tana nuna alhinin rasuwar Lawal, tare da mika ta’aziyya ga iyalansa da magoya bayansa.

Kano Pillars ta tura sakon ta'azziya
Kano Pillars, tsohuwar kungiyarsa a Najeriya, ita ma ta fitar da sanarwa, suna cewa mutuwarsa babban rashi ne ga masoya kwallon kafa, cewar Premium Times.
A baya an ce ya mutu ne a hatsarin babur a Entebbe Road, amma binciken ‘yan sanda ya nuna ya fado daga bene na kasuwa.
Saboda rashin fayyace gaskiya, ana kiran gwamnatin Najeriya da ta shiga tsakani don tabbatar da an gudanar da bincike mai zurfi.
Lawal ya koma Vipers SC a watan Yuli 2022 bayan ya shafe shekaru biyu yana taka leda a AS Kigali ta Ruwanda.
Yan kwallon Kano Pillars sun yi hatsari
Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sun yi hatsari a kan hanyarsu ta zuwa filin wasan Jos.
An ce tawagar Kano Pillars ta 'yan kasa da shekaru 19 ta yi hatsarin motar ne ranar Talata, 22 ga watan Oktobar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng