Kwallon Kafa: Hukumar NFF Ta Nada Sabon Mai Horas da Super Eagles

Kwallon Kafa: Hukumar NFF Ta Nada Sabon Mai Horas da Super Eagles

  • Ƙungiyar ƙwallon ƙafan Najeriya ta Super Eagles ta samu sabon wanda zai riƙa horar da ƴan wasanta a Najeriya
  • Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ta amince da naɗin Eric Sekou Chelle a matsayin sabon mai horar da ƴan wasan Super Eagles
  • Naɗin Eric Sekou Chelle wanda tsohon kocin ƙasar Mali ne, zai fara aiki ne nan take daga ranar Talata, 7 ga watan Janairun 2025

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin zartarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ya amince da naɗin Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, wato Super Eagles.

An yi naɗin ne bayan shawarar da kwamitin NFF ya bayar a wani taro da aka gudanar a Abuja ranar 2 ga watan Janairu, 2025.

Super Eagles ta yi sabon mai horaswa
NFF ta nada sabon mai horar da Super Eagles Hoto: Sia Kambou
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa naɗin ya samu amincewar kwamitin zartarwa na NFF a ranar 7 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin Miyetti Allah da aka kashe a shekara 5 da suka gabata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Eric Sekou Chelle?

Eric Sekou Chelle, mai shekara 47, tsohon kocin babbar ƙungiyar ƙwallon kafa ta Mali ne, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Yana da gogewa sosai, kasancewar ya jagoranci ƙungiyoyi irinsu GS Consolat, FC Martigues, Boulogne da MC Oran.

A lokacin da yake ɗan wasa a Faransa, Chelle ya bugawa ƙungiyoyi kamar Martigues, Valenciennes, Lens, Istres da Chamois Niortais.

An haifi Chelle a Côte d’Ivoire inda mahaifinsa yake ɗan ƙasar Faransa sannan mahaifiyarsa kuma ta kasance ƴar ƙasar Mali.

Ya cancanci wakiltar Côte d’Ivoire, Faransa da Mali, amma ya zaɓi bugawa Mali wasa, inda ya buga wasanni biyar kafin ya yi ritaya.

Sabon kocin Super Eagles ya taka rawar gani

A matsayinsa na kocin Mali daga 2022 zuwa 2024, Chelle ya jagoranci Aiglons zuwa wasan dab da na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirika (AFCON) ta 2023 a Côte d’Ivoire.

Mali ta kusa zuwa wasan kusa da na ƙarshe, amma ta sha kashi 2-1 a hannun Cote d'Ivoire bayan an yi ƙarin lokaci.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

A karkashin jagorancinsa, Mali ta yi nasara sau 14, ta tashi kunnen doki sau biyar, ta kuma sha kashi sau uku.

Zamansa kocin Mali ya ƙare a watan Yuni 2024, amma nasarorin da ya samu sun bar tarihi, ciki har da ɗaya daga cikin mafi kyawun wasanni da Mali ta yi a AFCON 2023.

Yaushe naɗin Chelle zai fara aiki a Super Eagles?

Super Eagles ta zama ba ta da mai horaswa bayan murabus ɗin Finidi George, biyo bayan rashin taɓuka abin kirki a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026.

Naɗin Chelle zai fara aiki nan take, kuma babban aikinsa shi ne jagorantar Najeriya wajen samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA na shekarar 2026.

Amorim ya zama kocin Man United

A wani tsohon labarin kuma, kun ji cewa Manchester United ta yi sabon mai horas da ƴan wasa bayan an sallami Erik Ten Hag daga bakin aiki.

Kara karanta wannan

PDP ta hango abin da zai faru idan ba ta karbi mulki ba a 2027

Kungiyar Manchester United ta naɗa tsohon kocin Sporting Lisbon, Ruben Amorim a matsayin wanda zai ci gaba ɗa horar da ƴan wasan kwallon kafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng