'Dan Najeriya Ta Lashe Kyautar Gwarzon Ɗan Kwallon Afirka na 2024
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na shekarar 2024.
Wannan kyauta da ɗan wasan mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Atlanta ya lashe, ta sa ya zama ɗaya daga cikin ƴan kwallon mafi hazaƙa a duniya.
Fitaccen ɗan jaridar nan da ya shahara a ɓangaren ƙwallon ƙafa, Fabrizio Romano ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.
Ɗan wasan gaba na tawagar ƙwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles ya lashe Ballon d'Or na Afika, watau gwarzon ɗan kwallom Afirka a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lookman ya samu nasara ne bayan ya shige gaban abokan karawarsa Ronwen Williams, Simon Adingra, Achraf Hakimi da kuma Serhou Guirassy.
"A hukumance, Ademola Lookman ya lashe kyautar Ballon d'or ta Afirka watau gwarzon ɗan kwallon ƙafa na nahiyar Afirka a 2024.
"Lookman ya samu wannan nasara kan abokan karawarsa, Ronwen Williams, Simon Adingra, Achraf Hakimi da kuma Serhou Guirassy."
- Fabrizio Romano.
Wannan nasara ta Lookman ta sa kyautar za ta ci gaba da zama a Najeriya bayan abokin wasansa a Super Eagles. Victor Osimhen ya lashe a bara watau 2023.
Asali: Legit.ng