Ten Hag: Jerin Masu Horaswa 5 da Ka Iya Maye Gurbin Kocin Manchester United

Ten Hag: Jerin Masu Horaswa 5 da Ka Iya Maye Gurbin Kocin Manchester United

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A jiya Litinin ne kungiyar ƙwallon kafa ta Manchester United ta sallami kocinta, Erik Ten Hag bayan ta sha kashi a hannun West Ham da ci 2-1.

Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne bisa la'akari da rashin nasarar da kocin ke yi, inda ya ci wasa huɗu kacal daga cikin wasanni 14 a kakar wasa ta bana.

Ruud van Nistelrooy, Thomas Franc da Xavi.
Jerin masu horarwan da ka iya maye gurbin Eric Ten Hag Hoto: Fabrizio Romano
Asali: Facebook

Manchester United ta kori Eric Ten Hag

Fitaccen ɗan jaridar nan, Fabrizio Romano ya tabbatar da korar kocin Man United a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu kungiyar kwallon ta fara zawarcin kocin da zai maye gurbin Ten Hag, na shida kenan bayan ritayar Sir Alex Ferguson.

Kara karanta wannan

Kopa 2024: Matashin ɗan kwallon Barcelona ya lashe babbar kyauta ta duniya

A watan Yuni, Ten Hag ya tabbatar da cewa United ta tuntubi wasu masu horarwa da nufin maye gurbinsa kafin ya amince da tsawaita kwantiragi.

Matsalar da Ten Hag ya samu a Man Utd

Tsohon kocin Ajax ya fara fuskantar matsin lamba bayan ya jagoranci Man United ta kare a mataki na 8 a teburin firimiya a kakar wasan bara, mafi muni tun 1992.

Nasarar da ya samu a gasar FA, kofi na biyu da ya lashe bayan Carabao Cup a 2023, ya sa mahukuntan Manchester United suka ƙara masa kwantaragin shekara guda.

Watanni uku bayan fara kakar wasan bana, United ta koma neman magajin Ten Hag. Legit Hausa ta tattaro maku masu horarwan da ka iya karbar aikin.

1. Kocin rikon kwarya, Ruud van Nistelrooy

Ba sabon abu ba ne a wurin Man United ta naɗa tsohon ɗan kwallonta a matsayin mai horarwa na wucin gadi a lokacin da take neman ɗaukar sabon koci.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ragargaji Tinubu, ya fadi yadda rashin wuta zai yi wa Arewa

Ryan Giggs, Michael Carrick, da Ole Gunnar Solskjaer duk sun riƙe matsayin kocin wucin gadi kuma daga bisani wasu daga ciki suka samu kwantiragin dindindin.

Van Nistelrooy na ɗaya daga cikin waɗanda ka iya maye gurbin mai horar da Man United idan har ya taka rawar gani a damar da ya samu yanzu.

An yi mamakin naɗin tsohon fitaccen ɗan wasan, lokacin da ya jingine burinsa na zama koci, ya karɓi aiki a matsayin mataimakin kocin Manchester United.

Ya buga wa United wasa daga 2001 zuwa 2006, inda ya zura kwallaye 150 a wasanni 219 da ya buga wa kungiyar kafin ya koma Real Madrid.

2. Tsohon kocin Ingila, Gareth Southgate

Tsohon kocin Ingila, Gareth Southgate na ɗaya daga cikin waɗanda kamfanin INEOS da daraktan wasannin United, Dan Ashworth ke hangen ya dace ya maye gurbin Ten Hag.

An yi tsammanin Southgate zai karɓi aikin kocin Man United ƙafin ya jagoranci tawagar ƴan wasan Ingila zuwa gasar cin kofin turai Euro 2024.

Kara karanta wannan

An fatattaki kocin Manchester United bayan ajiye munanan tarihi

Southgate ya bar aikin Ingila kwanaki biyu bayan ya sha kashi a hannun Spain da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin Euro 2024 kuma tun daga lokacin yake hutu.

3. Tsohon kocin Barcelona, Xavi Hernandez

Wasu majiyoyi a ƙasar Spain sun ce tsohon kocin Barcelona, Xavi ya fara tattaunawa kan yiwuwar komawa Old Trafford.

Xavi, wanda ya ci kofin duniya a 2010 yana da dangantaka ta kud-da-ƙud da shugaban zartarwa na United, Omar Berrada bayan zaman tare da suka yi Nou Camp.

A watan Janairu, Xavi ya yanke shawarar barin Barcelona a ƙarshen kakar wasan da ta wuce, amma daga bisani ya canza shawarar zai zauna.

Makonni bayan haka Barcelona da Xavi suka cimma matsayar cewa tsohon ɗan wasan tsakiyar zai bar ƙungiyar kuma tun wannan lokaci bai karɓi wani aiki ba har yanzu.

4. Kocin Brentford, Thomas Frank

Jaridar Talk Sport ta ruwaito cewa mahukunta Man United sun sa ido kan manajan Brentford, Thomar Frank.

Kara karanta wannan

Aikin dana-sani: Matashi ya shiga hannu bayan yin ajalin danginsa na kusa

Frank na daya daga cikin manyan kociyan gasar Firimiya a shekarun baya bayan nan duba da yadda jajirce ya riƙe Brentford a gasar tun bayan baro gasar gajiyayyu a 2021.

An danganta kocin da Chelsea a lokacin bazara bayan ƙungiyar ta raba gari da Pochettino, ko da yake Enzo Maresca ya maye gurbin daga karshe.

5. Kocin Sporting, Ruben Amorim

Fabrizio Romano ya wallafa rahoton cewa Man United ta tuntubi Rúben Amorím don maye gurbin Erik ten Hag.

Wakilan United sun fara tattaunawar farko da ƙungiyar kwallon kafa ta Sporting da ɓangaren kocin domin duba yiwuwar ɗaukarsa daga kungiyar.

A halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin kuma da yiwuwar Ruben Amorim ya zama sabon kocin Man United.

Lamine Yamal ya kafa tarihi a kwallon ƙafa

A wani rahoton kuma Lamine Yamal ya lashe kyautar gwarzon matashin ɗan kwallo watau Kopa Tropy 2024 a birnin Faris na ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

An yi nasarar gano matsalar lantarki a Arewa, TCN ya yi karin haske

Matashin ɗan kwallon wanda ke taka leda a Barcelona ya zama na farko da ya ci kyautar a ƙasa da shekaru 18.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262