Ballon D'Or: Dan Wasan Man City Ya Doke Vinicius, Ya Zama Gwarzon Ɗan Kwallon Duniya
- Rodri ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon duniya na maza watau Ballon D'Or 2024
- Ɗan wasan na tsakiya ya doke manyan abokan hamayyarsa, Vinicius Junior da Jude Bellingham na Real Madrid
- Rodri, ɗan kwallon Man City da Sifaniya ya taka rawar gani a kakar da ta wuce, ya lashe kofin firimiya da Euro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
France - Ɗan wasan tsakiya mai taka leda a Manchester City, Rodri ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon ƙafa na duniya wanda aka fi sani da Ballon D'Or.
Rodri ya doke manyan abokan karawarsa daga ƙungiyar Real Madrid ta ƙasar Sifaniya, Vinicius Junior da Jude Bellingham.
Fitaccen ɗan jarida, Fabrizio Romano ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook yau Litinin, 28 ga watan Oktoba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wata rana na faɗawa mahaifina, na bar kwallon kafa, buri na ba zai zama gaskiya ba amma sai ya faɗa mun cewa na ci gaba da jajircewa.
"Ya faɗa mani ka da na sare, na ci gaba da gwadawa har zuwa ƙarshe, yau ga shi ni ne a nan wurin, dole na gode maka (mahaifina)."
-Rodri.
Rodri ya kafa tarihin lashe Ballon D'Or
Dan wasan na kasar Sipaniya ya zama na biyu a gasar firimiya da ya lashe kyautar Ballon D'Or a shekaru 16 tun da Cristiano Ronaldo ya ci kyautar a 2008.
Rodri dai ya samu nasarori masu dumbin yawa a kakar wasan da ta wuce, inda ya ɗaga kofin Firimiya na ƙasar Ingila, UEFA Super Cup, FIFA Club World Cup da Euro 2024.
Yadda aka bada kyautar Ballon D'Or
Tun da Luka Modric ya lashe kyautar a shekarar 2018, Rodri shi ne dan wasan tsakiya na farko da ya lashe Ballon D'Or.
Daga wannan lokacin zuwa yanzu Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon D'Or yayin da Benzema na Reald Madrid ya samu kyautar sau ɗaya.
An kori kocin Man United
Rahotanni na nuni da cewa kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kori kocinta, Erik Ten Hag bayan shan kaye da suka yi.
Ana hasashen cewa an kori kocin ne bisa yadda kungiyar kwallon kafar Manchester United ta gaza tabuka abin kirki a bana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng