An Fatattaki Kocin Manchester United bayan Ajiye Munanan Tarihi
- Rahotanni na nuni da cewa kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kori kocinta, Erik Ten Hag bayan shan kaye da suka yi
- Ana hasashen cewa an kori kocin ne bisa yadda kungiyar kwallon kafar Manchester United ta gaza tabuka abin kirki a bana
- Ko a wasan karshe da Manchester United ta buga da West Ham a ranar Lahadi da ta wuce, kungiyar ta sha wani kaye mai ban ciwo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
London - Rahotanni da suka fito na nuni da cewa kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kori kocinta, Erik Ten Hag a yau Litinin.
A shekarar 2022 ne Erik Ten Hag ya fara aiki da Manchester United kuma a karon farko kusan ya tabuka abin kirki.
Rahoton BBC ya nuna cewa Manchester United ta fara shirin nada mukaddashin koci da zai rike kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kori kocin Manchester United, Ten Hag
Mirror ta ruwaito cewa kungiyar kwallon kafar Manchester United ta kori kocinta, Erik Ten Hag a yau Litinin, 28 ga watan Oktoba.
Erik Ten Hag ne kocin Manchester United na biyar tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson a shekarar 2013.
Dalilin korar kocin Manchester United
Ana hasashen cewa rashin tabuka abin kirki a kakar bana na cikin dalilan korar Erik Ten Hag daga Manchester.
Kungiyar Manchester United ta dawo ta 14 a teburin gasar Premier bayan shan kaye a ranar Lahadi da ta wuce.
Kokarin da Erik ya yi a Manchester Utd
A kakar wasan da ta wuce kungiyar Manchester United ta lashe kofin FA a karkashin jagorancin Erik Ten Hag.
Haka zalika a shekarar 2022 da Erik ya zo Manchester ya jagoranci kungiyar zuwa na uku a gasar Premier.
A yanzu haka dai kungiyar ta sanar da cewa Van Nistelrooy zai cigaba da jagorancin kungiyar kafin a samu koci na dindindin.
CAF ta hukunta Libya kan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa wulakanta 'yan wasan Super Eagles ya jefa kasar Libiya a cikin matsala yayin da CAF ta sanar da yanke hukunci.
Hukumar CAF ta ce ta kama Libiya da karya dokokin dokokin gasar cin kofin Afrika da kuma na CAF a abin da ta yi wa tawagar Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng