Kungiya Ta Fusata Tsohon Dan Wasan Barcelona, Ya Lale Kudi Zai Siye Ta Baki Daya

Kungiya Ta Fusata Tsohon Dan Wasan Barcelona, Ya Lale Kudi Zai Siye Ta Baki Daya

  • Tsohon dan wasan kwallon kafa ta Barcelona ya taya tsohuwar kungiyarsa ta Espanyol domin siyanta da makudan kudi
  • Martin Braithwaite ya fusata da irin wulakanci da kungiyar ta yi masa yayin da ya ke buga tamola kafin komawa Gremio
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Braithwaite na daga cikin 'yan wasan kwallon kafa da ke da tarin dukiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Barcelona, Spain - Tsohon dan wasan kungiyar Barcelona, Martin Braithwaite ya shiga rigima da kungiyarsa ta Espanyol.

Hakan ya biyo bayan sakinsa da suka yi a wannan kaka da muke ciki wanda hakan ya yiwa Braithwaite zafi matuka.

Tsohon dan wasan Barcelona zai saye kungiyar Espanyol saboda bata masa rai
Martin Braithwaite ya fusata da kungiyar Espanyol yadda suka mu'amalnace shi. Hoto: RCD Espanyol de Barcelona.
Asali: Facebook

Braithwaite ya fusata da lamarin Espanyol

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Football Espana ta ruwaito cewa dan wasan bai ji dadin yadda kungiyar Espanyol ta ke mu'amalantarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Braithwaite mai shekaru 33 ya yi yunkurin siyan kungiyar Espanyol gaba dayanta domin daukar fansar abin da ta yi masa da sauya shugabanninta.

Dan wasan ya tsaya a kungiyar tare da taimakonsu har suka sake haurawa zuwa gasar Laliga, cewar Goal.com.

Espanyol ta rabu da Braithwaite

Alaka ta kara tsami tsakanin Braithwaite da Espanyol wanda har ta kai suka dauki matakin sakinsa a matsayin wanda ba shi da kwantiragi da su.

Dan wasan gaban yana da tarin dukiya wanda ya mallaki babban kamfani a Amurka da ya kai $250m da wuraren cin abinci da shagon kayan sakawa da sauransu.

Cikas da Braithwaite ya samu a kwallo

Braitwaite wanda yanzu ya sanya hannu a kungiyar Gremio da ke Brazil ya sadaukar da rayuwarsa a Espanyol bayan ta samu koma baya a kakar bara.

Kara karanta wannan

Kano: An kama hatsabibin 'barawon' da ya fitini mutane da fashi zai tsere bayan sace N15m

Dan wasan na kasar Denmark ya ci karo da matsala bayan zuwa Barcelona inda ya gagara tabuka wani abu a kungiyar.

Daga bisani ya koma Espanyol inda nan ma bai yi abin kirki ba bayan buga tamola a Middlesbrougt da Leganes.

Messi ya yi magana kan ritaya

Kun ji cewa fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa a duniya, Lionel Messi ya bayyana kungiyar da zai ajiye tamola.

Messi ya ce zai yi ritaya ne a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami da ke buga gasar 'Major League Soccer' a kasar Amurka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.