'Yar Wasa ta Shiryawa Gasar Olympics a Faransa, Amma Najeriya ba Ta Yi Mata Rajista ba

'Yar Wasa ta Shiryawa Gasar Olympics a Faransa, Amma Najeriya ba Ta Yi Mata Rajista ba

  • Gwarzuwar 'yar wasan tsere a kasar nan, Favour Ofili ta zargi hukumomin wasannin Najeriya da yi mata bakin ciki
  • Misis Ofili ta ga laifin hukumar kula da wasannin Olympics ta Najeriya da hukumar kula da wasanni ta kasa kan kin shigarta gasar Olympics
  • Ta zarge su da cewa su ne su ka yi mata rajistar shiga gasar gudun fanfalakin mita 100 a wasannin da ke gudana a Paris ɗin Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - 'Yar wasan tseren Najeriya, Favour Ofili ta ɗora alhakin rashin shiga wasan tseren duniya na Olympics a kan mahukuntan Najeriya. Matashiyar 'yar tseren ta yi koken cewa hukumomin kasar nan ba su yi mata rajista a wasan gudun mai tsayin mita 100 ba.

Kara karanta wannan

Tana gama rera waka, fitacciyar jarumar Nollywood ta yanke jiki ta fadi matacciya

Ofili.fa
Yar wasan tsere ta zargi hukumomin wasannin Najeriya da kin sa sunanta cikin masu wakiltar kasar a gasar Olympics Hoto: Ofili.fa
Asali: Instagram

Favour Ofili ta wallafa a shafinta na Instagram cewa hukumar gasar Olympics ta Najeriya da hukumar wasanni ta kasa sun gaza yi mata rajista.

"Na cancanci shiga gasar Olympics," Ofiili

Gwarzuwar 'yar tseren Najeriya, Favour Ofili ta bayyana cewa ta cancanci shiga gasar tsere ta duniya (Olympics) da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Paris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta tattaro cewa Osili ta samu cancantar shiga gasar bayan ta zama gwarzuwar 'yar tsere ta kasa a gudun fanfalakin mita 100 a watan Afrilu.

Sai dai jami'ar Louisiana State University ta bayyana cewa babu sunan Mis Osili a cikin wadanda za su wakilci kasar a gasar wasannin duniya ta bana.

Ofili ta fusata da rashin sunanta a Olympics

'Yar wasan Najeriya ta fusata saboda rashin sunanta a cikin wadanda za su wakilci Najeriya a bangaren tseren gasar Olympics.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Favour Ofili ta bayyana cewa daga yanzu akwai shakku a cikin yadda hukumomin wasannin kasar nan ke tafiyar da ayyukansu.

Olympics: An kama 'yar Najeriya da kwaya

A wani labarin kun ji cewa Najeriya ta samu koma baya a gasar wasannin Olympics bayan an kama 'yar wasan damben kasar da shan kwaya mai kara kuzari.

Hukumomi sun gano kwayar furosomide mai kara kuzari a gwajin jini da aka yi wa yar wasan damben Najeriya, Cynthia Ogunsemilore, kuma an dakatar da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.