Ma'aikatar Wasanni Ta Kunyata Najeriya a Idon Duniya a Gasar Olympics, Tsohon Ministan Wasanni

Ma'aikatar Wasanni Ta Kunyata Najeriya a Idon Duniya a Gasar Olympics, Tsohon Ministan Wasanni

  • Tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, Salomon Dalung, ya soki ma'aikatar wasanni
  • Dalung yace babu yadda za'a yi a rushe hukumomin da suka ɗau shekaru suna shirya yan wasa kuma a yi tunanin nasara
  • A cewarsa tawagar yan wasan Najeriya sun je yawon buɗe ido ne Japan da kuma kunyata Najeriya

Abuja - Tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, Barista Salomon Dalung, ya bayyana cewa ma'aikatar wasanni ta ɓatawa Najeriya suna a idon duniya.

Dalung yace ministan wasanni ya kwashi tawagarsa zuwa kasar Japan domin yawon shakatawa da kuma kunyata Najeriya amma ba don gasar Olympics ba.

Tsohon ministan ya yi wannan tsokaci ne a wata fira da Legit.ng Hausa ranar Litinin 9 ga watan Agusta.

Barista Salomon Dalung
Ma'aikatar Wasanni Ta Kunyata Najeriya a Idon Duniya a Gasar Olympics, Tsohon Ministan Wasanni Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hasashen Dalung tun kafin fara gasar Olympics

Tun a baya, tsohon ministan ya yi hasashen cewa Najeriya ba zata iya taɓuka komai ba a gasar Olympics da zata halarta.

Dalung ya yi wannan hasashen ne bisa matakin da ministan wasanni, Sunday Dare, ya ɗauka na rushe hukumomin wasanni a Najeriya.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

Da aka tambayeshi ko ya akai ya iya hango nesa, Dalung yace:

"Ita gaskiya bata neman sutura kuma gaskiya ta na tafiya a sirrince ne don haka sai wanda Allah ya yi masa gyaɗan dogo na ganin gaskiya kuma zai dauki kasadar faɗin gaskiyan."
"Ni a yadda Allah ya halicce ni, kowane wayewan gari abinda nake nema a wurin Allah shine, kafin inyi shahada na tsaya a kan turba madaidaiciya, amma ba abinda zai biyamun bukata ba."

Wane shiri ka yi tun bayan wasan 2016?

Dalung ya bayyana cewa tun bayan da suka dawo daga Olympics ta 2016 ya fara shirye-shiryen sanya Najeriya alfahari a gasa ta gaba 2020.

Acewarsa ko da lokacin ba shine a matsayin minista ba, idan aka cigaba da tsarin zaiyi tasiri sosai.

Barista Dalung yace:

"Gasar Olympic bayan shekara 4 ake yi, lokacin da nike minista bayan mundawo daga gasar Olympics 2016, na ɗau gagarumin tsari na tabbatar da cewa idan Allah ya kaimu 2020,"

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista

"Kuma ko ina nan ko bana nan idan aka cigaba to Najeriya zata yi tasiri a wannan wasannin da ake yi."
"Na farko na tabbatar da cewa kungiyoyin wasannin waɗanda sune ginshikan buga wasa, na tabbatar da cewa kowane ɗan wasa an horar da shi, bayan haka an tabbatar yana bin dokokin kiwon lafiya na shiga gasa."

Na shigo da matasa cikin harkar wasanni

Barista ya kara da cewa ya kuma fahimci cewa mafi yawan yan wasan Najeriya sun gaji, alal misali Osonoke wacce take buga gasar Table Tennis.

A cewarsa ta wakilci Najeriya a gasar Olympics hudu babu wani abu da ta yi na azo a gani.

Dalung yace:

"Sai na farfaɗo da wasannin matasa wanda muka fara a 2016 har zuwa 2019 lokacin da na bar ofis, a wannan lokaci mun zakulo yan wasan da a wasan Olympic na gaba za'a yi rigima da mu."
"Mun shirya musu wasannin sada zumunta daban-daban kuma sun ciyo zinare da azurfa, munje wasan Olympics na matasa a Argentina sun nuna bajintarsu kwarai kuma sun bawa Najeriya kyakkyawan suna."

Kara karanta wannan

Haramun ne: Wani dalibi ya gina gunkin Aisha Yesufu, aikinsa ya jawo cece-kuce

"Amma sai gashi wata ɗaya kafin Olympics 2020 minista ya rushe wannan kungiyoyin. Wannan yasa an canza waɗanda suka ɗau shekaru suna shirya yan wasa."

Yace wannan yasa na faɗawa yan Najeriya cewa abinda minista yayi kuma babu wanda ya dawo da shi kan hanya ya nuna cewa Najeriya ba ta shirya wasan Olympics ba.

Shin canza alkalin wasa gab da wasa zai kawo Alheri?

Daga karshe ministan yace tawagar yan wasan Najeriya sun je Japan yawon buɗe ido ne da kuma kunyata Najeriya.

Yace:

"A ganina Najeriya taje yawon buɗe ido ne Japan kuma an durkushe burin yaran mu. Mutum 10 da aka kora an sanya musu lahani."
"Saboda haka abinda muka je yi Japan, mun je wasan borin bada kunya ne amma ba wasa muka je ba."

A wani labarin kuma sabon rahoton da aka fitar na jerin masu kudin duniya ya nuna cewa Dangote ya koma na 117

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Attajirin Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

Rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin 'Dangote Group' ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.

Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262