An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Tsohon Dan Wasan Bayern Munich Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Tsohon Dan Wasan Bayern Munich Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An shiga jimami bayan rasuwar dan wasan kwallon kafa ta Bayern Munich da Inter Milan, Andreas Brehme a kasar Jamus
  • Marigayin wanda ya zura kwallon da ta bai wa kasar Jamus nasara a wasan karshe a shekarar 1990 a gasar kofin duniya
  • Har ila yau, Brehme ya lashe kofuna da dama a kungiyoyin kwallon kafar Kaiserslautern da Bayern Munich da Inter Milan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Berlin, Jamus – Tsohon dan wasan kasar Jamus, Andreas Brehme ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 63.

Brehme shi ne ya zura kwallon da ta bai wa kasar Jamus nasara a wasan karshe na cin kofin duniya a shekarar 1990, cewar Goal.com.

Kara karanta wannan

Wasan karshe na AFCON: Gaskiyar batu kan bidiyon da ke zargin golan Ivory Coast da sanya guraye

Fitaccen dan wasan kwallon kafa ya riga mu gidan gaskiya
Andreas Brehme ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 63. Hoto: Anreas Brehme.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rasu?

Marigayin ya yi nasarar buga wasanni 86 inda ya samu damar zuwa kwallaye takwas ga kasar Jamus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Brehme ya yi nasarar lashe kofuna da dama a kungiyoyin kwallon kafar Kaiserslautern da Bayern Munich da Inter Milan.

Kungiyar Bayern Munich ita ta sanar da mutuwar fitaccen dan wasan a yau Talata 20 ga watan Faburairu., Cewar Sky Sports.

Sanrwar Bayern Munich tace:

“Kungiyar Bayern Munich ta kadu da mutuwar bazata na dan wasan Jamus, Andreas Brehme.
“Za mu ci gaba da rike Andreas Brehme a cikin zuciyarmu, a matsayinsa na wanda ya lashe gasar kofin duniya wanda ya kasance na musamman.
“Zai kasance kullum a cikin ‘yan wasan da ke da martaba a kungiyar kwallon kafa na Bayern Munich, Ubangiji ya masa rahama.”

Nasarar da Brehme ya samu

Kara karanta wannan

Kano: Fitaccen dan kasuwa, Dantata ya fadi tsarin mulki da ya fi dacewa da Najeriya, ya fadi dalili

Brehme ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa na Kaiserslautern daga shekarar 1981-68 da kuma 1993 zuwa 1998.

Har ila yau, ya yi nasarar lashe kofin Bundesliga a shekarar 1998 da kuma ‘German Cup’ a shekarar 1996.

Daga bisani kuma marigayin ya jagoranci kungiyar a matsayin koci daga shekarar 2000 zuwa 2002.

Musa ya magantu kan makomarsa

Kun ji cewa Kyaftin din Super Eagles, Musa Ahmed ya yi magana kan makomarsa yayin da aka kammala gasar AFCON.

Musa ya ce ko a yaushe a shirye ya ke a matsayinsa na dan kwallo a ko wane lokaci zai amsa gayyata idan aka kira shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.