Ivory Coast Ta Lashe AFCON: Duk Da Kokarin Da Ta Yi Da Farko, Najeriya Ta Sha Kaye a Wasan Karshe

Ivory Coast Ta Lashe AFCON: Duk Da Kokarin Da Ta Yi Da Farko, Najeriya Ta Sha Kaye a Wasan Karshe

  • Ivory Coast ta zama zakara gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2024, bayan galaba kan Najeriya
  • Ivory Coast ta lashe wasan da 2 - 1 bayan sha da kyar inda aka kusa fitar da ita a matakin 'group stage'
  • 'Yan Najeriya da dama wadanda zukatansu suka karaya sun nuna rashin jin dadinsu a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Bayan tubaka kokari sosai har suka kai wasan karshe, Super Eagles ta Najeriya ta sha kaye hannun Elephants na Ivory Coast.

Najeriya ta doke Afirka ta Kudu inda ta kai wasan karshe, hakan yabawa Super Eagles damar karawa da Elephants na Ivory Coast, masu masaukin baki.

'Yan Najeriya da dama wadanda zukatansu suka karaya sun nuna rashin jin dadinsu a dandalin sada zumunta.

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta wallafa rubutu a karshen wasan. Duba abin da ta wallafa a kasa:

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164