Innalillahi: Ɗan Wasan Kwallon Najeriya Musulmi Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Filin Atisaye, Ya Rasu
- Innalillahi, wani ɗan wasan kwallon ƙafa, Sodiq Adebisi, ya faɗi kasa ana tsaka da atisaye a filin kwallo a jihar Ogun
- Rahotanni sun bayyana cewa bayan hanzarta kai shi Asibiti, ɗan wasan ya rasu a ranar Asabar a garin Ijebu-Ode
- Hukumar yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce danginsa sun nemi a ba su gawar su masa jana'iza a Musulunce
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Wani ɗan kwallo a Najeriya mai suna, Sodiq Adebisi, ya riga mu gidan gaskiya yayin da je ɗaukar horo tare da sauran ƴan wasa a jihar Ogun.
Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa ɗan wasan ya rasu ne jim kaɗan bayan ya yanke jiki ya faɗi a filin wasan 'Dipo Dina International Stadium' da ke garin Ijebu-Ode.
Yadda lamarin ya faru ana tsaka da atisaye
Ɗan wasan mai kimanin shekaru 34 ya shiga atisaye tare da abokansa 'yan wasan kwallon kafa a ranar Asabar da ta gabata, kwatsam ya faɗi ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta tataro cewa ganin yadda Adebisi ya fadi kasa, nan take abokan wasansa suka garzaya da shi asibitin jihar da ke Ijebu-Ode.
Duk da namijin kokarin da ma’aikatan asibitin suka yi domin ceto rayuwarsa, Sodiq ya rasu a ranar da aka kwantar da shi.
Bayanai sun tabbatar da cewa a halin yanzu an aje gawar marigayin a ɗakin ajiyar gawarwaki na jihar Ogun da ke garin Ijebu-Ode.
Danginsa sun ba su bukatar a yi bincike
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin ga ƴan jarida.
Odutola ya bayyana cewa ɗan uwan marigayi ɗan kwallon mai suna, Ganiyu Adebisi, ya je ofishin 'yan sanda na Igbeba domin ya karɓi gawarsa su rufe shi.
Kakakin yan sandan ya ce:
"Ɗan uwansa ya je caji ofis din yan sanda na Igbeba domin ba da rahoton abin da ya faru. Danginsa sun faɗa mana ba su son a yi wani dogon bincike."
"Sun bayyana cewa burinsu kawai a ba su gawarsa su masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."
MURIC ta nemi a gudanar da bincike
A wani rahoton kare hakkin Musulmi (MURIC) ta maida zazzafan martani kan kisan da sojoji suka yi wa masu Maulidi a jihar Kaduna.
MURIC ta bukaci Gwamnatin Bola Tinubu ta gudanar da bincike mai zurfi kuma a hukunta duk wanda aka kama da hannu a harin Tudun Biri.
Asali: Legit.ng