'Yan Sanda Sun yi Ram da Magoya Bayan Arsenal 8 kan Murnar Lallasa ManChester United
- Jami'an tsaro a kasar Uganda sun cafke matasa 8 magoya bayan Arsenal da suka bazama kan tituna sun murnar nasarar da kungiyar ta samu kan Man U
- Matasan 8 sanye da rigunan kungiyar kwallon kafan sun kwashi har motoci biyar suna murna tare da shagali a birnin Jinja da ke Uganda inda kwatsam 'yan sanda suka cafke su
- Duk da kakakin rundunar 'yan sandan yace matasana basu san koma kan kungiyar ba a tambayoyin da suka yi musu, yace basu nemi izini ba kafin fara murnar
Uganda - Jami’an tsaro a Jinja da ke Uganda sun damke magoya bayan Arsenal takwas kan shagalin murnar nasarar cin kungiyar Manchester United 3 da 2 a Premier League.
Kamar yadda Daily Monitor, wata jaridar Uganda ta bayyana, an kama masu murnar a ranar Litinin bayan kwasar tawagar motoci biyar suna shagalin murna a fadin garin.
Wadanda aka kama din suna sanye ne rigar kungiyar kwallon kafan tare da alamar kofin, jaridar TheCable ta rahoto
A ranar Lahadin da ta gabata ne Arsenal ta lallasa Manchester United a wasan da suka buga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin jawabi kan kamen, Baker Kasule, wanda ke cikin kungiyar, yace suna murna ne kan nasarar kungiyarsu yayin da aka cukuikuyesu zuwa caji ofis.
“Ban san me muka yi ba amma muna murna ne kan nasarar kungiyar mu da ta samu kan abokiyar hamayya Manchester United.”
- Kasule yace.
Sai dai, James Mubi, kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Kira, yace magoya bayan Arsenal din sun yi zagayen ne ba tare da amincewar jami’an tsaro ba.
Yayi ikirarin cewa kungiyar ta bayyana rashin sanin muhimman abubuwa game da kungiyar kwallon kafan wanda ya saka tantama a kan manufarsu.
“Mun tambaya sunan kocin Arsenal, yawan kungiyoyin premier league, yawan wasannin da Arsenal ta buga, yawan nasarorinsu da faduwarsu a wannan kakar da kuma manyan zakarun kungiyar hudu amma babu amsa.
“Basu dan komai a kan Arsenal ba, shiyasa ba mu damu da cewa magoya bayan Arsenal bane.”
- Mubi yace.
An tattaro cewa, an saki magoya bayan Arsenal din bayan kwashe kwana daya a caji ofis.
Kudi kare magana: Ronaldo na neman kwararren kuku da zia dinga biya N2.5m duk wata
A wani labari na daban, fitaccen 'dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo na neman wanda ya kware a girki don daukarsa aiki.
Zai dinga yi masa girki tare da iyalansa a sabon katafaren gidansa da ya gina a Portugal wanda za a gama a watan Yuni.
Asali: Legit.ng