Mahaifiyar Pele Mai Shekara 100 Ba Ta San Ya Mutu Ba, In Ji Yar Uwarsa
- A baya-bayan nan ne fitaccen dan kwallon kasar Brazil da ya shahara a duniya, Pele, ya riga mu gidan gaskiya, kuma al'umma da manyan mutane na ta ta'aziyya
- Sai dai bayan rasuwarsa, yar uwarsa mai suna Maria Lucia do Nascimento ta ce har yanzu mahaifiyarsa ma bata san ya mutu ba
- Maria Lucia ta ce mahaifiyarsu, Celeste Arantes, wacce ta haura shekaru 100 a duniya tana rayuwa ne a wani duniyanta na daban don ko an fada mata abu bata cika fahimta ba
Brazil - Maria Lucia do Nascimento, yar uwar Pele, ta ce mahaifiyar dan kwalon kafar na kasar Brazil ba ta san gogaggen dan kwalon, kuma danta ya rasu ba.
A cewar Mirror UK, Maria Lucia, yar shekara 78 kuma yar uwar Pele tilo wacce ke raye, ta yi magana ne a wani hira da aka yi da ita a Brazil.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Pele, wanda aka saba yi wa lakabi da 'Sarkin Kwallon Kafa', ya rasu a ranar Alhamis bayan fama da kansar ciki.
Tun bayan hakan, mutane da dama sun yi ta mika sakon ta'aziyya tare da alhini daga bangaren yan kwallo da sauran al'umma.
Mahaifiyar Pele ta ba ta san danta ya mutu ba
Duk da alhinin rashinsa da ake yi a fadin duniya, Maria Lucia ta ce har yanzu mahaifiyar 'ba ta an halin da ake ciki ba'.
Ta kara da cewa dattijuwan wacce ta haura shekaru dari 'tana wani duniyanta ne' ba tare da cikakkiyar masaniya game da labarin ba, rahoton The Cable.
Yar uwar ta Pele ta ce:
"Muna magana amma ba ta san halin da ake ciki ba. Tana duniyanta ne na daban."
"Ta bude idonta da na ambaci sunansa kuma na ce 'za mu masa addu'a,' amma ba ta san abin da na ke cewa ba."
Celeste Arantes ta haifi Pele a 1940 a Tres Coracoes, wani birni da ke kudu maso gabashin Brazil.
Shine babban cikin yayanta uku, da suka hada da Zoca - ya mutu a 2020 - da Maria Lucia.
Mahaifiyar Pele da farko bata goyi bayan ya zama dan kwallo ba
Da farko Celeste ba ta goyon bayan rungumar kwallo a matsayin sana'a da Pele ya yi saboda rashin nasara da mahaifinsa ya yi a kwallon, har tana masa fada idan ya sulale ya tafi buga kwallo.
Amma daga bisani ta amince ta saka masa albarka bayan an ta rokonta.
Asali: Legit.ng