Bayan Fafatawa Tsawon Mintuna 120, Ajantina Sun Lashe Kofin Duniya

Bayan Fafatawa Tsawon Mintuna 120, Ajantina Sun Lashe Kofin Duniya

  • Bayan wata guda ana taka leda a kasar Larabawa, gasar kwallon duniyar Qatar 2022 ya zo karshe
  • Ajantina da Faransa sun taka leda mai cike da tarihi a wasan karshe na gasar kwallon ta bana
  • Shugaban kungiyar FIFA, Infantino, ya bayyana cewa wannan shine mafi kyau a tarihin gasar kwallon duniya

Qatar - Bayan fafatawa da kai ruwa rana tsakanin yan kwallon kasar Faransa da kasar Ajantina na tsawon mintuna 120, wasa ya zo karshe.

Yan kwallon Ajantina sun lashe gasar kwallon kofin duniya na shekarar 2022 a kasan Qatar bayan shekaru 36.

Ga yadda wasar ta gudana:

Minti na 23 - Messi ya ci kwallom farko ta Fenariti

Minti na 36 - Angel Di Maria ya zura kwallo ta biyu ragar Faransa

MInti na 80 - Mbappe ya rama kwallo daya ta Fenariti baya ture Kolo Mani da akayi

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minti na 81 - Mbappe ya zura kwallo ta biyu

Minti na 108 - Lionel Messi ya kara kwallo daya

Minti na 118 - Mbappe ya sake ramawa kuma kwallonsa ta uku

Ajantina
Bayan Fafatawa Tsawon Mintuna 120, Ajantina Sun Lashe Kofin Duniya
Asali: Twitter

Wasa ya kare aka shiga fenariti

Bugun farko - Mbappe 1 : Messi 1

Bugun biyu - Kingley Coman na Faransa ya zubar, Paulo Dybala na Ajanta ya ci

Bugun Uku - Tchoumeni na Faransa ya zubar, Paredes na Ajantina ya ci

Bugun 4 - Kolo Muani ya ci, Montiel na Ajantina kuma ya zuwa ci muje gida

Tarihi

Rabon da Ajantina ta lashe gasar kofin duniya tun shekarar 1986 lokacin zamanin Diego Maradona.

Yan Ajantina sun lashe gasar kofin duniyar farko a 1978 inda suka lallasa Netherlands 3-1. Sannan suka lallasa Jamus a 1986 da ci 3-2.

Asali: Legit.ng

Online view pixel