Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022

Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022

  • Sabon dan wasan Bayern Munich Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022.
  • Yar wasar kwallom kafa na Najeriya da Clob din Barcalona Asisat Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar kwalon kafa ta Africa na 2022
  • Edouard Mendy dan wasan Senegal da Mohamed Salah na kasar Masar suka yi gasar lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Afrika - Dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal kuma sabon dan wasan Clob din Bayan Munich Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022. Rahoton BBC

Karo na biyu kenan Sadio Mane yake lashe kyautar gwarzon kwallon kafa na Nahiyan Afrika, bayan da ya lashe a 2019 daga nan ba a kara gudanar da bikin ba saboda barkewar cutar korona.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: EFCC Ta Gurfanar Da Dakataccen Akanta Janar Na Tarayya A Gaban Kotu Kan Zambar N109bn

Cikin wadanda suka yi takarar gasar gwarzon kwallon kafa na Nahiyar Afrika sun hada Edouard Mendy dan wasan Senegal da clob din Chelsea da kuma Mohamed Salah na kasar Masar da Clob din Liverpool.

MANE S
Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022 FOTO SI
Asali: Getty Images

Yar wasar kwallon kafa na Najeriya da Clob din Barcalona Asisat Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar kwalon kafa ta Africa na 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karo na biyar kenan da Asisat Oshoala ke lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta Nahiyar Africa.

Matan da suka yi takarar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta shekarar 2022 da Asisat Oshoala sun hada da Ajara Nchout Njoya ta Kamaru da Inter Milan da Grace Chanda ta Zambia da BIIK Kazygurt.

Ronaldo ya na neman yin kwantai, kungiyoyi 5 sun ki sayen ‘Dan wasan Man Utd

A wani labari kuma, Cristiano Ronaldo yana neman rasa kungiyar da zai bugawa kwallon kafa yayin da ake ta rade-radin yana neman barin Manchester United.

Kara karanta wannan

Lissafi ya Kwacewa Najeriya, Bashin da Ake Biya ya fi Karfin Kudin da Ake Samu

Sports Brief ta kawo rahoto manyan kungiyoyin Turai irinsu Paris Saint Germain da Bayern Munchen sun ki yarda su dauki hayar ‘dan wasan gaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel