Kwallon kafa: Daga zuwan sabon Koci ya shiga tarihi, Najeriya ta doke kasar Sao Tome 10 – 0
- Najeriya ta je har kasar São Tomé and Príncipe inda ta buga wasa na biyu na zuwa gasar AFCON
- ‘Yan wasan Super Eagles sun doke São Tomé and Príncipe da ci 10-0 a filin kwallon kafa na Agadir
- Idan Super Eagles su ka cigaba da wannan kokari, za su samu damar zuwa kasar Moroko a 2023
São Tomé - ‘Yan wasan kwallon kafan Najeriya na Super Eagles sun samu maki uku masu tsada yayin da suka hadu da kasar São Tomé and Príncipe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an buga wasan na samun zuwa gasar nahiyar AFCON a babban filin nan na Grand Stade Agadir da ke kasar Sao Tome.
Victor Osimhen ya zura kwallaye hudu a raga a wannan wasa wanda shi ne na biyu. Hakan yana nufin Najeriya ta samu maki shida daga wasanni biyu.
Kafin nan Super Eagles ta doke Sierra Leone a filin wasan MKO Abiola na birnin Abuja a Najeriya inda a nan ma Osimhen ne ya yi sanadiyyar yin nasara.
Punch ta ce tun a minti na biyu Najeriya ta fara kai hari, amma sai a minti na tara ‘dan wasan gaban Napolin ya iya leka ragar Anastacio Braganca.
A minti na 19 da 23 Terem Moffi da Osimhen sun yi yunkurin zura kwallo a ragar kasar adawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk kokarin mai tsaron ragar watau Braganca, karyarsa ta kare a minti na 28, Aina ya kawowa Osihmen kwallon da shi kuwa ya gara ta ga Moses Simon.
An yi wa Sao Tomo raga-raga
Ba za a ce masu masaukin bakin ba su yi abin kirki ba, rahoton ya ce a minti na 32, Luis Leal ya nemi jefa kwallo a ragar Francis Uzoho, amma bai dace ba.
Channels ta ce ragowar kwallon ‘dan wasan gaban Super Eagles sun zo ne a mintina na 48, 62 da 84.
Kowa ya ci na shi
Terem Moffi ya ci kwallaye biyu, yayin da Oghenekaro Etebo, Simon Moses, da kuma Ademola Lookman duk suka samu damar zura kwalla guda a wasan.
Daf da za a tashi aka shigo da ‘dan wasan gaban kungiyar Watford, Emmanuel Dennis bai bar filin ba sai da ya tabbata ya ci wa Najeriya kwallonta na goma.
Alkawari ya cika
Kwanakin baya rahoto ya zo cewa Gwamnatin Tarayya ta yarda ta raba gidaje ga ‘yan wasan Super Eagles da suka yi wa Najeriya kwallo a shekarar 1994.
Shugaba Muhammadu Buhari ya tuno da tsohon alkwarin da aka yi wa taurarin. Shekaru kusan 30 kenan ba a cika wannan alkawari ba sai a gwamnatin nan.
Asali: Legit.ng