UCL: Burina mu hadu da Real Madrid, mu rama abin da ya faru a shekarar 2018 inji Salah

UCL: Burina mu hadu da Real Madrid, mu rama abin da ya faru a shekarar 2018 inji Salah

  • Mohammed Salah ya bayyana yunuwarsa na sake haduwa da kungiyar Real Madrid a gasar UCL
  • ‘Dan wasan gaban na Liverpool zai so ya rama abin da ya faru a wasan karshe na shekarar 2018
  • Real Madrid ta doke kungiyar Ingilan a birnin Kiev bayan Sergio Ramos ya ji wa Mo' Salah rauni

Villareal - ‘Dan wasan gaban Liverpool, Mohammed Salah ya bayyana sha’awarsa na gwabzawa da Real Madrid a wasan karshe na cin kofin Turai.

ESPN ta rahoto Mohammed Salah a ranar Talata yana cewa zai fi jin dadin haduwa da zakarun Sifen watau Real Madrid a maimakon Manchester City.

Salah ya zanta da ‘yan jarida ne bayan kungiyarsa ta Liverpool ta samu galaba a kan Villareal a wasan daf da karshe a gasar cin kofin na nahiyar Turai.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

Tauraron zai so Real Madrid ta doke Man City a wasan da za ayi a birnin Madrid a ranar Laraba.

2018 zai maimaita kansa

Idan Madrid sun iya doke Manchester City a wasansu na karshe, za a gwabza tsakanin kungiyar ta Sifen da Liverpool kamar yadda aka yi a kakar 2018.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shekaru hudu da suka wuce, Real Madrid ta doke Liverpool da ci 3-1, amma Salah bai samu buga wasan da kyau ba, a sakamakon rauni da ya samu a kafada.

Salah
Mohammed Salah Hoto: www.football365.com
Asali: UGC

Wannan karo ‘dan wasan na kasar Masar zai so ya sake samun dama a kan Real Madrid domin ya rama abin da Sergio Ramos da kungiyarsa ta yi masu.

“City kungiya ce mai wahalar karawa, mun yi wasa da su babu laifi a shekarar nan. Idan aka tambayi ra’ayina, zan fi son Madrid.” - Mohammed Salah.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Da aka tambayi Salah ko zai so ya huce takaicin rasa kofi a hannun Real Madrid, sai ya nuna haka ne.

“Mun rasa wasan karshe a hannunsu, saboda haka ina so mu yi wasa tare da su, sannan mu na sa ran mu yi nasara a kan su.” - Mohammed Salah.

Liverpool tayi waje da Villarreal

Goal.com ta ce ‘dan wasan gaban ya yabi kwazon da abokan wasansa su ka nuna a karawarsu da Liverpool, su ka dawo daga baya su ka doke Villareal.

Fabinho, Luis Diaz da Sadio Mane su ka zura kwallo bayan an fara cin Liverpool kafin hutun rabin lokaci.

Kareem Benzema na tashe

A watan Maris aka ji labari Karim Benzema ya ci kwallaye uku a zagayen wasansu da PSG. Bayan nan ya zurawa Chelsea da Manchester City kwallaye a raga.

A dalilin haka, yanzu Benzema ne ‘dan kwallo mafi tsufa da ya taba cin kwallaye uku a wasa daya a tarihin gasan Turan, kwallayensa a gasan Turan sun haura 40.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng