Matasa sun fara lalata filin kwallon Abuja sakamakon kashin da Najeriya ta sha hannun Ghana
- Yan wasan Najeriya Super Eagles sun sha kashi hannun kasar Ghana a gida brnin tarayya Abuja
- Wannan rashin nasara ya fusata yan Najeriyan da suka yi tattaki filin kwallo don kallon wasan
- Yanzu haka matasa sun bazama cikin filin kwallo sna lalata duk abinda suka gani
Abuja - Wasu matasa yan Najeriya da suka je kallon kwallon Najeriya da Ghana a filin kwallon Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja sun fusata, sun haukace.
Wani dan jaridan Ghana, Yaw, ya dauki bidiyon matasa da yammacin nan sun bazu cikin filin kwallon bayan waje da Najeriya da kasar Ghana tayi kuma ta hanata zuwa gasar kwallon duniya a Qatar bana.
Bidiyon ya nuna jami'an tsaron sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa matasan amma da alamun abun ya yi kamari.
Kalli bidiyon:
Ghana ta haramtawa Najeriya shiga gasar cin kofin duniya
An tashi daga wasan share fagen shiga gasar kofin duniya da za a yi Qatar, wanda Super Eagles ta Najeriya ta buga da kasar Ghana a yau Talata.
Wannan na nuni da cewa, Najeriya ta fice daga gasar ta neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karshen wannan shekara, bayan da ta yi kunnen doki (1-1) da Ghana, inda ta sha kashi idan aka jimillar maki.
Wannan shi ne karo ba biyu da Najeriya ta buga wasa da Ghana, inda a bakon jiya 'yan wasan Najeriya suka yi tattaki zuwa kasar Ghana, kamar yadda muka ruwaito a baya.
Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), ta kori Augustine Eguavoen daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan gazawar da Super Eagles ta Najeriya ta yi na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2022, bayan da suka tashi kunnen doki da Black Stars ta kasar Ghana a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja ranar Talata.
Asali: Legit.ng