Da Duminsa: Bayan Ahmed Musa, Wani Ya Sake Yi Wa Tsohon Dan Wasan Super Eagles Kyautar Naira Miliyan 1
Tsohon mai tsaron bayan ya bayyana matsin rayuwa da ya shiga a baya-bayan nan wadda hakan yasa ya fara amfani da motarsa kirar Sienna domin yin kabu-kabu ya ciyar da iyalansa.
Mr Ujoma, wanda shine shugaban LuckyBay Estate and Properties Limited, ta tabbatarwa Premium Times bada tallafin a safiyar ranar Asabar.
Ya ce ya bada tallafin ne ga Obiekwu saboda ya tausaya masa halin da ya shiga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mr Ujomu ya ce:
"Da na ji labarin, na tuntube shi domin sanin sahihancin labarin. Sun aika min da lambar sa (Obiekwu) da lambar asusun bankinsa. Kawai sai na ce bari in tallafa masa da kudin."
Dan kasuwan ya ce yana daga cikin masoyan dan kwallon a lokacin da ya ke buga wasa.
Kyautar ta Mr Ujoma na zuwa ne kwanaki biyu bayan Kyaftin Super Eagles, Ahmed Musa, ya bawa tsohon dan wasan tallafin Naira miliyan 2.
Ba zan ce komai ba game da tallafin, Obiekwu
Da aka tuntube shi, Obiekwu ya ki tabbatar da tallafin yana mai cewa ya yanke shawarar sirrinta duk tallafin aka bashi sai zuwa wani lokaci gaba, Premium Times ta rahoto.
Kocin na Ingas FC, ya ce ya ji kunya a ranar Juma'a yayin da yan wasansa suka fara rokonsa ya basu kudi cikin N2m da Ahmed Musa ya bashi.
Mr Obiekwu ya ce:
"Bana son in yi magana a kan lamarin. Bana son yin magana kan kudaden da aka bani kada masu garkuwa su sace ni ko iyalai na. A karshe zan yi wa yan Najeriya godiya kan abin da suka min."
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng