Jerin Koci 8 da aka sallama daga aiki yayin da Cristiano Ronaldo ke taka leda a karkashinsu
- Cristiano Ronaldo, ɗan wasan kwallon kafa ne da ya shahara a duniya wajen kafa tarihin zura kwallaye, kuma ya taka leda a kungiyoyi da dama
- Mun tattaro muku jerin masu horarwa 8 da suka rasa aikin su yayin da ɗan wasan ke murza leda a karkashin su
- A jiya ne dai, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami Ole bayan shan kashi a hannun Watford
Ɗan wasan gaba na kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa da ake ji da su a duniya, wanda suka haɗa da Juventus, Real Madrid da Sporting Lisbon.
Zakakurin ɗan wasan wanda ya shahara a fagen tamaula a Duniya, ya saba nuna kansa a kowane wasa da ya taka, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Legit.ng Hausa ta haɗa muku jerin sunayen wasu masu horar wa da suka rasa aikin su yayin da ɗan wasan ke taka leda a karkashin su.
1. Manuel Pellegrini a Real Madrid
Mai horarwa Pellegrini ya jagoranci tawagar yan wasan Real Madrid na tsawon wasanni 48 tsakanin watan Yuni 2009 zuwa Mayu 2010.
2. Jose Mourinho a Real Madrid
Kocin wanda ake kira da, "Chosen One" Mourinho ya raba gari da kungiyar Real Madrid ne cikin ruwan sanyi bayan gaza lashe gasa ko guda ɗaya.
Jose ya jagoranci kungiyar a wasanni 178, tsakanin watan Mayu 2010 zuwa watan Yuni 2013.
3. Carlo Ancelotti a Real Madrid
Ancelotti ya rasa aikinsa ne a kungiyar Real Madrid bayan ya jagoranci kungiyar daga watan Yuni 2013 zuwa Mayu 2015 a wasanni 119.
Kocin ya bayyana cewa jagororin ƙungiyar sun fara tantama akan nagartarsa, kuma ya faɗi haka ne a jawabin da ya fitar a wancan lokacin.
4. Rafa Benitez a Real Madrid
Bayan wasanni 25 a matsayin kocin Real Madrid da kuma kashin da ya sha a hannun abokiyar hamayya Barcelona da ci 4 babu ko ɗaya, an sallame shi nan take.
5. Sarri a kungiyar Juventus
Bayan Maurizio Sarri ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta ƙasar Italiya ta lashe gasar Seria A sau 9 a jere, cire kungiyar daga gasar zakarun turai da Lyon ta yi ya yi sanadin sallamarsa daga bakin aiki.
6. Pirlo a Juventus
Tsohon ɗan wasan Juventus ɗin ya karbi ragamar kungiyar daga hannun Maurizio Sarri, a watan Agusta 2020.
Ya jagoranci kungiyar ta lashe kufunan Coppa Italia da kuma Suppercoppa Italiana amma ya kare a mataki na 4 a teburin gasar Seria A.
Juventus ta sallame shi bayan gaza lashe gasar kofin League na kasar Italiya karo na farko a tsawon shekara 10, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
7. Ole Gunnar Solskjaer a Manchester United
Na karshe da ya faru kwanan nan, shine matakin sallamar koci Ole Gunnar Solskjaer da kungiyar Manchester United ta ɗauka.
OGS ya rasa aikinsa ne bayan ya sha kashi a hannun kungiyar Watford 4-1 a filin wasa na Vicarage Road ranar Asabar.
Kazalika kungiyar Liverpool ta zura wa yan wasan OGS kwallaye 5 a raga, yayin da abokiyar hammayyarta da suke gari Man City ta zura wa United kwallo biyu da nema.
A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga
Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa ɗan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a fagen zura kwallo uku a wasa ɗaya.
Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura kwallo uku rigis a wasa ɗaya yayin da yake wakiltar ƙasa.
Asali: Legit.ng