Jihar Zamfara
An ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma a kusa da kauyen Kucheri da ke Tsafe, inda maharan suka yi wa motoci kwanton bauna tare da bude masu wuta.
Rundunar sojojin kasar nan ta jaddada matsayarta na kai farmaki har maboyar yan ta'addan da su ka addabi jama'a, musamman a Arewa maso Yammacin kasar nan.
Gwamnan jihar Zamfara ya saki fursunoni 31 kuma ya musu kyautar N50,000. An saki fursunonin ne saboda yawan kama yan bindiga. An saki fursunonin domin rage cunkoso.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare babban titin hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara. Tsagerun sun kashe muum biyu tare da yin garkuwa mutane masu yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da ke atisayen Hadarin Daji sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda biyar tare da raunata wasu da dama a karan battar da suka yi.
Mazauna Anka a jihar Zamfara sun yi ihun neman dauki biyo bayan barazana da yan bindiga su ka yi na kai masu hari saboda cafke dan ta'adda a yankin.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi 14 da ake da su a jihar.
Rikici ya balle tsakanin dabar Gurgun Daji da wata dabar daban, wanda ya jawo hallaka daya daga cikin jagororin yan ta'adda da su ka addabi mazauna Zamfara.
'Yan bindiga sun kai hari kan matafiya a jihar Zamfara. Daga cikin wadanda harin ya ritsa da su har da shugaban rundunar tsaro ta Askarawan Zamfara.
Jihar Zamfara
Samu kari