Gwamna Bello Matawalle Ya Yi Wa Fursunoni 39 Afuwa a Jihar Zamfara

Gwamna Bello Matawalle Ya Yi Wa Fursunoni 39 Afuwa a Jihar Zamfara

  • Gwamnatin Gwamna Mohammed Bello Matawalle na jihar Zamfara ta yi wa wasu fursunoni 39 afuwa a fadin jihar
  • Fursunonin da aka yiwa afuwar sune wadanda kotunan shari’a na jihar suka yanke musu hukunci tare da tsare su a gidan yari a Gusau
  • An yafe wa fursunonin ne bayan shawarar da kwamitin jin kai karkashin jagorancin Atoni Janar na jihar ya bai wa ofishin Gwamna

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa fursunoni 39 da aka yankewa hukunci kan laifuffuka daban-daban a gidan gyara hali na Gusau, babban birnin jihar.

Da yake aiwatar da sakin fursunonin, Matawalle ya ce wannan na daga cikin shirin jin kai na gwamnatinsa a fadin sassan jihar, PM News ta rahoto.

Gwamna Bello Matawalle
Gwamna Bello Matawalle Ya Yi Wa Fursunoni 39 Afuwa a Jihar Zamfara Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Matawalle wanda ya samu wakilcin Atoni Janar na jihar, Alhaji Junaidu Aminu, ya bayyana cewa an fara shirin afuwan ne tun a watan Maris din shekarar nan inda wani kwamiti da Atoni Janar din ke jagoranta ya tantance fursunonin.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

Gwamnan ya yi bayanin cewa fursunonin da suka koyi kyawawan halayya kawai sune suka ci gajiyar wannan shiri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An zakulo fursunonin daga bangarori daban-daban

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rahoto cewa kwamitin ya zabi fursunoni 46 da aka yanke wa hukunci daban-daban, ciki harda masu daurin watanni shida da daurin shekaru 20.

Hakazalika akwai wasu fursunoni 11 da aka yankewa daurin rai da rai sannan wasu biyar da aka yankewa hukuncin kisa.

Daga cikin fursunonin da aka tantance, an saki 30 da aka yankewar daurin watanni shida zuwa shekaru 20 da wasu tara da aka yankewa daurin rai da rai. An kuma rage hukuncin kisa da aka yankewa wasu biyar zuwa daurin shekaru bakwai a gidan yari.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda aka yiwa afuwan da su kasance jakadu nagari a cikin al’ummarsu tare da yi musu gargadin kada su sake aikata wani laifi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Karar Zabe Ta Fatattaki Segun Oni, Tace Oyebanjin APC ne Ya Lashe Zaben Ekiti na Gwamna

Wasu da aka yiwa afuwa, sun sha alwashin zama mutane nagari tare da mara wa dukkan manufofin gwamnati da shirye-shiryenta na cigaban jihar baya, rahoton Vanguard.

A wani labari na daban, wasu guggun yan ta'adda sun yi garkuwa da babban limamin kauyen Masama-Mudi da ke Zamfara, saboda wa'azi da ya ke yi game da yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel