Albashin ma'aikata
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyoyin kwadago da su hakura da shirinsu na tsunduma yajin aiki saboda kasa cimma matsaya a kan mafi karancin albashi.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Nyesom Wike ya yi a karshen mulkinsa inda ya zargi rashin bin tsari a daukar ma'aikatan.
Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ayyana fara yajin aiki daga ranar Litinin mai zuwa kan gazawar gwamnati a batun mafi ƙarancin albashi da kuɗin wuta.
Shugaban TUC na kasa, Festus Osifo ya ce ƴan kwadago za su iya saukowa ƙasa daga bukatarsu ta biyan N494,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
Majalisar wakilan tarayya ƙarƙashin jagorancin Tajudeen Abbas ta lashi takobin gudanar da bincike kan yadda CBN ke korar ma'aikata barkatai da sunan gyara.
Gwamnatin tarayya ta kungiyoyin kwadago za su koma teburin tattaunawa domin sake duba kan batun mafi karancin albashi da yake ta yamutsa hazo a kasar nan.
Kwamitin dake tattaunawa kan mafi karancin albashi har sai baba ta gani ba tare da bayyana dalilin hakan ba. Kungiyar kwadago dai ta ki amincewa da tayin gwamnati.
Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta roki kungiyoyin NLC da TUC kan suyi hakuri su karbi N60,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Kungiyoyin kwadago na Najeriya sun sake yin fatali da sabon mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar. Sun bukaci a rika biyan ma'aikata N494,000.
Albashin ma'aikata
Samu kari