Taraba
Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cafke dan ta'addar da ya fitini kauyuka a jihar Taraba. Dan ta'addan, Ibrahim Hassan ya amsa laifinsa a hannun jami'an tsaro.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya nuna adawarsa da kiran da ake yi na a samar da 'yan sandan jihohi a kasar nan. Gwamnan ya ce jami'an tsaron da ake da sun isa.
Tsadar abinci na kokarin hana mutane sayan ragunan sallah a birnin Jalingo da ke jihar Taraba. Dillalan raguna sun koka kan rashin kasuwa duk da kokarin da suke.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare a kauyukan jihar Taraba. 'Yan bindigan sun hallaka mutum 11 a farmakin wanda suka kai da sanyin safiya.
Hajiya Lami Adamu Lau, shugabar kungiyar mata ta ƙasa ta kwanta dama a lokacin da ta je jihar Kebbi domin gudanar da wasu ayyuka, gwamnan Taraba ya yi alhini.
Al’umar kauyen Usmanu dake karamar hukumar Karim Lamido sun wayi garin Litinin cikin kunci da tsoro bayan wasu’yan bindiga sun kutsa garinsu a daren Lahadi.
Sojojin Najeriya sun kama yan bindiga a Wukari da Ibi a jihar Taraba, yan bindigar sun ba sojojin cin hancin N2m domin a sake su amma sojojin sun ki yarda.
Matsalar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas ya kara ƙamari yayin da mutanen yankin suka bukaci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi murabus.
Wasu gungun 'yan banga sun yi ajalin wani babban jami'in ɗan sanda, ASP Tapu Godfrey a kauyen Sardauna da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Taraba
Samu kari