Kudu maso gabashin Najeriya
Cif Ikechukwu Nnadi wanda aka fi sani a Andy Best, shahararren mai shirya fina-finai a Najeriya ya mutu a wani asibitin Owerri, babban birnin jihar Imo.
Yayin da 'yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali, ashe wasu gwamnoni su na shan wahala bayan Gwamna Charles Soludo ya ce ya shafe shekaru biyu ba tare da albashi ba.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charlse Soludo ya caccaki wani shugaban karamar hukuma a jihar kan rashin kula da aikin da aka saka shi a yankinsa.
Miyagin ƴan bindiga sun kashe yan sandan da ba su gaza biyar ba a titin Hilltop, a babban birnin jihar Ebonyi ranar Jumu'a, 8 ga watan Maris, 2024.
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya tura sakon jaje ga fitattun sarakunan gargajiya uku a jihar kan rasuwar matansu inda ya ce mutuwar da abin takaici.
Mafi yawan gwamnoni na korafi kan yadda suke samun jiharsu bayan tsohuwar gwamnati ta sauka, Gwamnan Abia ya magantu kan yadda ya samu tashi jihar.
Yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027, Da alamu Tinubu ba zai sake tsayawa takara ba yayin da ake neman kawo dokar da za ta hana wasu yankuna takara.
Sunday Igboho ya sha suka, Fulani sun nemi jami'an tsaro su kame shi bayan da ya dawo daga tsare da aka yi a kasar waje kan wasu dalilai na shiga kasa ba lasisi.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin yan kungiyoyin asiri ya yi ajalin dalibi ɗaya yayin da wasu da dama suka ji raunuka a jami'ar fasaha ta tarayya FUTO.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari