Kungiyar Manoman Shinkafa
A labarin nan za a ji yayin da ƴan kasuwa ke zargin junansu da kawo tasgaro wajen hauhawar farashin shinkafa, kasuwar Singa a Kano ta ce komai ya daidaita.
Ambaliya ta lalata gonakin shinkafa a garuruwa 7 na jihar Kebbi, inda dubban manoma suka yi asara yayin da ake fargabar samun karancin abinci a ƙasar.
Rahoton SBM Intelligence ya nuna sauyin yanayi da rashin tsaro sun lalata noma a Najeriya, inda ambaliya da zaizayar ƙasa suka shafi miliyoyin mutane da gonaki.
Abdul Samad Rabiu ya ce rage haraji daga gwamnati ya taimaka wajen rage farashin abinci, inda shinkafa ta faɗo daga N110,000 zuwa N60,000 a kasuwanni.
Farashin buhun shinkafa ya sauka zuwa N58,000 a Najeriya sakamakon shigo da shinkafar Indiya ta barauniyar hanya daga Jamhuriyar Benin zuwa kasuwannin kasar nan.
A kasuwar hatsi ta Potiskum da ke jihar Yobe, wake ya yi tashin gwauron zabi yayin da farashin masara, dawa da gero suka sauka. Ana sayar da shinkafa kan N51,000.
NAFDAC ta kama buhuna 120 na jabun shinkafa a Rivers, inda ta kai su ofishinta na Kudu maso Kudu, ta kuma kama wata mata tare da kayan hada jabun shinkafar.
Gwamnatin tarayya ta ce jama'a su kwantar da hankulansu, inda ta ƙaryata cewa akwai tsoron ƙasa za ta iya faɗawa a cikin ƙarancin abinci a ƴan kwanaki masu zuwa.
Jihar Jigawa da ke fama da matsanancin rikicin manoma da makiyaya ta fara kokarin hada kan bangarorin biyu domin tabbatar da an daina zubar da jinin jama'a.
Kungiyar Manoman Shinkafa
Samu kari